Saudiyya: Me yasa askarawa ke tsaron limaman Makka?

Sheik Abdul Rehman Al Sudais a lokacin da yake jan sallah a masallacin Ka'aba Hakkin mallakar hoto Facebook/HaramainSharifain
Image caption Sheik Abdul Rehman Al Sudais a lokacin da yake jan sallah a masallacin Ka'aba

Shafin Facebook na masallatan Ka'aba da na Madina a Saudiyya, ya yi karin haske a kan dalilan da ya sa askarawa ke gadin limaman masallatan har a lokacin da suke jan sallah.

Hakan ya biyo bayan yawan tambayar da mutane ke yi na neman sanin ko me ya sa askarawan ke bai wa limaman masallatan masu tsarki guda biyu tsaro.

Shafin ya yi bayani game da dalilan, inda ya ce a shekarun baya limaman na shiga su fita daga masallatan ba tare da askarawa sun yi gadinsu ba, sai bayan da wasu abubuwa suka faru sannan aka dauki matakan sanya askarawa su ba su tsaro

Sanarwar ta zayyana wasu manyan dalilai guda uku da ta ce su ne suka jawo hankalin hukumar masallacin;

  • Akwai lokacin da wani mutum ya tunkari Sheikh Ali Al Hudaify yana ihu a dai-dai lokacin da limamin ke jan sallar Asuba a shekarar 2015.
  • Haka kuma wani mutum ya ture Sheikh Juhany, sannan mutumin ya fara ihu a makirifo a lokacin da limamin ke jan sallar Azahar a shekarar 2011.
  • Yayin da wani mutum ya yi yunkurin soka wa Sheikh Sudais wuka a lokacin da yake zaman tahiya a masallacin Ka'aba da ke Makka a karshen shekarun 2000.
Hakkin mallakar hoto Haramain
Image caption Sheikh Khalid Al Muhanna na daya daga cikin limaman Harami

Haka kuma tasirin dandalin sada zumunta a duniya ya sa mutane sun san fuskokinsu, don haka ya sa ake sanya askarawa su basu kariya daga taron jama'a da kuma kaucewa irin wadannan abubuwan da suka faru a baya.

Haka zalika, mahajjata da dama kan yi kokarin rungumar limaman sakamakon shaukin kaunar ganin su, inda wasu kan yunkurin taba gemu domin neman tabaraki.

Askarawan da ke kare limaman da ma wadanda ke tsayawa cikin masu bin sallah, su kan yi tasu sallar ce bayan an kammala sallar jam'i.

Hakkin mallakar hoto Haramain
Hakkin mallakar hoto Haramain
Hakkin mallakar hoto Haramain

Labarai masu alaka