An yanke wa mutum 16 hukuncin kisa kan kisan daliba

Nusrat Jahan Rafi

Asalin hoton, family handout

Bayanan hoto,

An bulbula kananzir a kan Nusrat sannan aka cinna mata wuta

Wata kotu a Bangladesh ta yanke wa mutum 16 hukuncin kisa kan kona wata daliba bayan zargin hedimastanta da neman lalata da ita.

Nusrat Jahan Rafi, mai shekara 19 dai ta mutu a watan April a garin Feni, wani dan kauye mai tazarar kilomita 160 a wajen birnin Dhaka.

Mutanen da aka yanke wa hukuncin kisan sun hada da malamin da Nusrat ta zarga da neman lalata da ita da kuma wasu mata biyu 'yan uwanta dalibai.

Malamin dai ya yaudari Nusrat zuwa kan soro a ranar 6 ga watan Afrilu 2019, inda kuma bayan kwana 11 ne da faruwar al'amarin Nusrat ta kai malamin nata kara ofishin 'yan sanda cewa ya tattaba mata jiki.

Daga nan ne sai wasu mutum biyar masu sanye da burqa suka yi mata kawanya inda suka nemi da ko dai ta janye korafin nata ko kuma su dauki mataki a kanta.

Nusrat ta ki janye karar, al'amarin da ya sa nan take mutanen suka cinna mata wuta kuma hakan ne ya yi sandiyyar mutuwarta daga bisani.

'Yan sanda sun ce makasan na Nusrat sun so juya al'amarin ya yi kama da kisan kai to amma sai ta samu ta tsira.

Kisan Nusrat dai ya girgiza jama'a a fadin Bangaledash inda jama'a suka yi ta zanga-zangar neman a hukunta makasan nata.