Yadda sojojin sama suka 'kashe' mutane a Sokoto

Hafsan sojojin sama

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar sojin saman ta Najeriya ta tabbatar da faruwar al'amarin a daren Lahadi da ta gabata, inda ta ce tana bincike a kai.

Bayanai dai sun nuna cewa wasu samari ne a unguwar Mabera da ke birnin Sokoto suka tsokani wata matashiya wadda saurayinta soja ne.

Matashiyar ta fusata da tsokanar da aka yi mata inda ta kira saurayin nata domin ya daukar mata fansa.

Daga nan ne kuma sojan ya gayyato abokan aikinsa inda da zuwansu wurin suka sanya mutanen da budurwar sojin ta yi kara gwale-gwale.

Wani wanda aka harba a kafa mai suna Sulaiman Aliyu ya shaida wa BBC cewa sojojin sun lakada musu dan karen duka.

"Daga zuwan sojojin sai suka fantsama suna bin jama'a da duka da harbi inda wani yaro da suka biyo ya zo ya rungume ni yana cewa don Allah malam ka taimake ni ka da ka bari su wuce da ni."

Sulaiman ya ci gaba da cewa "hakan ne ya sa sojojin suka yi ta kokarin saka ni da yaron a cikin motarsu, ni kuma da na ji dukan da suke yi mana ya yi yawa sai na yi kokarin shiga wani gida."

"Shiga gidan ne ya sa sojan ya harbe ni da bindiga a kafata inda harsashin ya fita ya samu wata mace mai ciki al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar matar."

Sai dai kuma rundunar sojan saman ta bakin mai magana da ita, Air Commodore Ibikunle Daramola ta shaida wa BBC "an yi wa jami'anta rauni ta hanyar amfani da wuka".

Tuni dai gwamnatin jihar Sokoto ta sha alwashin ganin an hukunta duk wadanda aka samu da laifi a al'amarin.