'Tabbas Adam Zango ya biya 46m domin karatun marayu'

Adam Zango

Asalin hoton, Instagram/Adam Zango

Bayanan hoto,

Adam Zango ya biya wa 'yan makarantar sakandare miliyoyin naira don ci gaba da karatunsu

Shugaban makarantar Professor Ango Abdullahi da ke birnin Zariya, Dr Shamsuddeen Aliyu Maiyasin, Garkuwar makarantar Zazzau, ya ce babu tantama kan naira miliyan 46 da fitaccen dan wasan Hausan nan, Adam Zango ya zuba a makarantar domin tallafa wa marayu 101 su yi karatu.

Dr Shamsuddeen ya kara da cewa ba wannan ne karon farko ba da fitaccen jarumin yake bayar da irin wannan gudunmawa ba ga marasa karfi musamman kan abin da ya shafi karatunsu.

Latsa wannan alamar lasifikar da ke kasa domin sauraron hirar Dr Shamsuddeen Aliyu da Haruna Ibrahim Kakangi.

Bayanan sauti

Dr Shamsuddeen Aliyu

A ranar Laraba ne dai Adam Zango ya wallafa batun tare da rasitin biyan kudin a shafinsa na Instagram.

Wannan batu ne dai ya janyo mahawara a kafafen sada zumunta, inda da dama ke ganin Adam Zango ba shi da kudin da zai iya biya wa marayu 101 kudin makaranta na shekara uku.

To sai dai BBC ta tuntubi wasu na kusa da jarumin inda suka shaida mata cewa "yana da gidauniya da ke neman tallafin mutane musamman masu hannu da shuni."