Na dimauce kan mutuwar budurwata da ta kashe kanta saboda ni

Mutum a cikin damuwa

Asalin hoton, Getty Images

Saurayin yarinyar da ta mutu bayan ta cinna wa kanta wuta a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ya ce yanzu a yanzu yana ganin rayuwarsa ta baci dalilin rasa masoyiyarsa.

Umar Labaran, mai shekara 25 ya ce ya dimauce kan rasuwar budurwar tasa mai suna Aisha wadda ta kona kanta a watan da ya gabata bayan ya gaza kawo kudin neman aurenta.

Aisha ta rasu ne a ranar Laraba bayan fama da jinya ta fiye da wata guda sakamakon raunukan da ta samu bayan cinna wa kan nata wuta.

Umar ya ce "Damuwata yanzu na rasa ta kuma ba zan sake samun wadda zata maye min gurbinta ba, da wuya in samu wadda za ta maye min gurbinta."

Ya ce sun kwashe kusan shekara biyu suna soyayya, kuma sun hadu ne a lokacin da take tallar gyada shi kuma yana kabu-kabu sai ya ganta ya ce yana son ta.

Kafin rasuwarta, Aisha ta shaida wa BBC cewa ta dauki matakin kashe kanta ne saboda ba za ta iya hakura da saurayin nata ba kuma "da ta yi karuwanci gara ta kashe kanta" kawai.

Mahaifin Aisha Aminu Muhammad Albarkarawa ya shaida wa BBC cewa saurayi ne take so tsawon shekara daya amma Allah bai sa yana da abin aurenta ba.

"Saboda haka ne muka dakatar da shi da zuwa wurinta tunda ba shi da abin aurenta har sai Allah ya kawo mata wani.," in ji Aminu Muhammad.

Ya kara da cewa: "Ashe ita kuma tana sonsa sosai. Shi ne ta dauki wannan mataki ba tare da saninnmu ba, kawai sai ganinta muka yi tana ci da wuta, jama'a suka yti kokarin wutar.