An shirya wa masu ciki taron motsa jiki a bainar jama'a

Mata masu ciki da suka shiga wani sabon tsari na motsa jiki a bainar jama'a a Rwanda sun shaida wa BBC cewa sun ji dadin tsarin kuma suna son hukumomi su ci gaba da yi.
Sama da mata dari ne suka halarci taron na farko a Kigali, babban birnin Rwanda a karshen makon da ya wuce. Masu shirya motsa jikin sun ce fatansu shi ne "a sauya yadda ake kallon jikin mace mai jiki."
Nelson Mukasa, shugaban wata kungiya mai zaman kanta da suka fara taron motsa jikin, ya ce mutane da yawa a Rwanda sun yadda cewa da zarar mace ta dauki ciki dole ne ta daina duk wani aikin motsa jiki.
"Ya kamata mutane su gane cewa rashin motsa jiki ga mai ciki na da hadari ga jikinta da dan da take dauke da shi," in ji Mista Mukasa.
Ana kammala motsa jikin, Libérée Uwizeyimana- mai dauke da cikin wata takwas- ta shaida wa BBC cewa bata taba motsa jiki ba a lokacin da take da ciki.
"Duk na gaji saboda ban saba ba, amma kuma ina farin ciki da na motsa jiki tare da wasu matan masu ciki," ta ce.
Ruth Ntukabumwe, wadda ke dauke da ciki wata bakwai ta ce tana so ta ci gaba da motsa jikinta.
"Abu ne mai kyau, Na motsa jiki, na samu natsuwa kuma motsin da dan cikina ke yi ya sa na ji dadi sosai," a cewarta.
Dakta Jean Nyirinkwaya, wata likitar mata a Kigali ta bayar da shawarar cewa duk wata mace mai ciki da ke zuwa asibitinsa ta rika motsa jikinta.
"Tafiya da ninkaya da mika ba su da wata illa a gare su," in ji Dakta Nyirinkwaya.
Masu shirya taron motsa jikin sun ce sun zabi salo-salo na motsa jiki da ba su yi wa matan illa ba. Sun kuma gayyaci maza don su rako matansu a lokacin motsa jikin.