An tsinci gawar 'yan China 39 cikin babbar mota a Ingila

Bayanan bidiyo,

Bidiyon motar da aka gano gawarwakin 39

'Yan sanda sun ce gawarwaki 39 da aka gano a bayan wata babbar motar a birnin Essex na Ingila 'yan kasar China ne.

A yanzu 'yan sanda na ci gaba da yi wa direban motar Mo Robinson mai shekaru 25 tambayoyi bisa zargin kisan mutanen da suka hada da mata tara da maza 31.

Jami'ai a Ireland ta Arewa sun kai samame kan wasu gine-gine uku yayin da suke neman 'ya'yan wata kungiya da ake zargin na da hannu a lamarin.

Tirelar ta so ne daga Zeebrugge a Belgium an kuma kama ta a Purfleet da ke kusa da tekun Thames na Burtaniya.

Wani ma'aikacin motar agaji ne ya gano gawarwakin da misalin karfe daya da rabi na ranar Laraba, bayan da tirelar ta bar Purfleet da misalin karfe 1: 05.

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto,

Sunan direban babbar motar Mo Robinson, dan yankin County Armagh

A yanzu an killace babbar motar a wani wuri na daban ya yin da ake cigaba da binciken musabbabin mutuwar wadanda ke ciki.

Rundunar 'yan sandan Essex ta sanar da cewa wannan shine bincike mafi girma da ta taba yi a tarihi, ta kuma tabbatar da cewa mutanen yan kasar Chana ne.

Sanarwar ta kara da cewa binciken musabbabin mutuwar mutanen 39 wani jan aiki ne da zai dauki lokaci.

Jekadan Chana a Burtaniya Liu Xiaoming ya rubuta kalaman alhini a shafinsa na Twitter, inda yace suna kan tattaunawa da hukumar 'yan sandan Burtaniya.

Bayanan bidiyo,

"Na ga mutane na ta fitowa da gudu daga cikin motar"

Da farko 'yan sanda sun ce babbar motar ta fito ne daga Bulgaria, kafin ta fahimci cewa ta shigo ne Burtaniya daga Belgium .

Mai magana da yawun ma'aikatar kasashen wajen Belgium ya ce an yi wa motar rajista ne kawai a kasar, amma mallakar wani dan kasar Ireland ce.

Kawo yanzu ba a iya gano yaushe aka jibge gawarwakin a cikin babbar motar ba.

A cewar Lucy Moreton ta kungiyar ma'aikatan hukumar shige da ficea burtaniya, irin yadda kwantenoni ke tururuwa zuwa Burtaniya ya sa ba za'a iya duba dukkanin kayan da su ka dauko ba.

Lucy Moreton ta kara da cewa akwai bukatar isassun kayan aikin bincikar irin wadannan kwantenoni da ke daukar manyan kaya.

To amma ma'aikatar cikin gida ta ce tana binciken manyan motoci da kuma kwantenoni ta yin amfani da hanyoyin fasaha na zamani.

Bayanan hoto,

An bude rijistar ta'aziyya a Cibiyar Thurrock

An gudanar da zaman makoki da yammacin Laraba a harabar ofishin ma'aikatar cikin gida, inda aka yi kira ga hukumomi da su samar da hanya mafi sauki ga wadanda ke gujewa yaki da talauci za su iya shiga Burtaniya don neman mafaka.

Bayanan bidiyo,

CCTV ta nuna yadda motar ta tsaya a babbar tasha

Ko a shekarar 2000, an gano gawarwaki 58 na yan cirani daga kasar Chana a bayan wata babbar mota a Dover.

Hakama a shekarar 2015, 'yan sanda sun gano gawarwaki 71 a bayan wata babbar motar da su ke tunanin masu safarar mutane a yankin Bulgaria da Hungary ne su ka kwaso su.