An sake kai samame makarantar mari a Adamawa

'Yan sandan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Karo na biyar kenan eda ake kai samame kan makarantun mari a arewacin Najeriya

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa a Najeriya ta ce ta kai samame wani gida da ta ce makarantar horar da kangararru ce, inda ake tsare da mutum 15, biyu daga cikinsu kananan yara.

Wannan ya biyo bayan irin wannan samame da aka yi a garuruwan Kaduna da Katsina da Daura.

Wani mai magana da yawun 'yan sanda ya shaida wa BBC cewa samamen ya biyo bayan wani tsaigumi ne da suka samu.

Wasu daga cikin wadanda aka kubutar din sun bayyana cewa ana tsare da su ne cikin kaskanci sannan kuma ana ba su abinci sau daya a rana.

Daya daga cikinsu ya ce ya wayi gari ne a gidan kangararrun bayan ya bukaci a ba shi gadon mahaifinsa da ya rasu.

Tuni aka garzaya da mutum biyu daga cikinsu asibiti domin yin magani ga raunukan da suka ji.

Kazalika, an kama mai makarantar tare da 'ya'yansa guda biyu. 'Yan sanda sun ce sun fara bincike da nufin gano 'yan uwan wadanda aka kubutar.

Wannan ne karo na biyar da 'yan sanda ke kai samame a kan makarantun mari a cikin wata guda a Arewacin Najeriya.