Shirin Gane Mani Hanya: Yadda bikin #BBCHikayata na 2019 ya gudana

Shirin Gane Mani Hanya: Yadda bikin #BBCHikayata na 2019 ya gudana

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron shirin Gane Mani Hanya game da bikin na Hikayata

A jiya Asabar ne aka karrama gwarazan gasar kagaggun labarai ta BBC Hausa ta mata zalla wato Hikayata, inda Safiyya Ahmad ta zo ta daya da labarinta mai suna "Maraici". An ba ta kyautar dala 2,000.

Jamila Abdullahi Rijiyar Lemu ce ta zo ta biyu da labarinta mai suna "Ba a Yi Komi Ba," wacce ta karbi kyautar dala 1,000.

Sannan labarin "A Juri Zuwa Rafi" na Jamila Babayo shi ne ya zo a matsayi na uku, wadda ta karbi kyautar dala 500.