'Babu shirin yin magudi a zaben Nijar'

Mahamadou Issofou

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar zaben jamhuriyar Nijar ta CENI ta musanta zarge-zargen cewa ana shirin yi magudi a zaben kasar da ke karatowa.

A baya-bayan nan ne ake ta yada jita-jita a shafukan sada zumunta na cewa hukumar ta shirya rijistar masu zabe ta boge a wasu wurare a kasar, inda wasu suka rika cewa sun ga na'urori a wuraren da bai dace a gansu ba.

Amma hukumar ta ce bahaguwar fahimta wasu suka yi wa aikin.

Mataimakin shugaban hukumar Aladuwa Amada ya ce "lokacin da aka ce an gano wasu suna kidaya na bogi, akwai wasu na'urori da suka lalace sai da aka gyara, bayan an gyara kuma dole a gwada a tabbatar suna aiki shi ne aka je wasu kauyukan Yamai uku aka je aka gwada.

"Wannan ne ya sa mutane suke gani kamar ana toge," in ji shi.

Ya ce kuma za a goge sunan mutanen da aka je aka yi gwajin rajistar da su a kan na'urorin kafin lokacin zaben.

Tun a ranar 15 ga wannan watan ne aka fara rajistar masu zaben a jihohin kasar hudu, sai dai wasu na ganin cewa har yanzu ma'aikatan hukumar CENI ba su lakanci na'urorin rajistar na zamani ba.

Amma hukumar ta ce ta horas da ma'aikatanta sosai don gudanar da wannan aikin kuma ba rashin iya sarrafa na'ura ba ne ke jawo tafiya hawainiya a aikin rajistar.

A watan Disambar 2020 ne a ke sa ran yin zagayen farko na zaben shugaban kasar da na 'yan majalisar dokoki.