An dakatar da likita don an haifi jariri ba fuska a Portugal

Stock image of doctor carrying out an ultrasound

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana ci gaba da bincike kan likitan

An dakatar da wani likitan mata a Portugal bayan da wata mata ta haifi jaririnta ba hanci da idanuwa da wani bangare na kokon kansa.

Iyayen jariri Rodrigo ba su da masaniyar irin nakasar da dansu ke da ita sai da aka haife shi a farkon watan nan.

Jami'ai a majalisar likitoci sun yanke shawarar dakatar da Dakta Artur Carvalho bisa zargin wasa da aikinsa.

An gano cewa an sha yin korafi tun a baya dangane da wasu jariran.

Wannan ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar bayan da kafofin yada labaran Portugal din suka watsa labarin.

Dakta Carvalho bai ce uffan ba kan zarge-zargen har yanzu kuma BBC ba ta samu damar magana da shi ba.

Me ya samu jariri Rodrigo?

An haifi Rodrigo ran 7 ga watan Oktoba a asibitin São Bernardo da ke Setúbal a kudancin Lisbon.

Mahaifiyarsa ta samu kulawa ne daga Dakta Carvalho tun da ta samu ciki kuma iyayen sun ce likitan bai taba nuna masu wata damuwa kan lafiyar jaririn ba, duk da ya sha yin hoton cikin.

Mahaifiyar ta ce an yi hoton cikin ta sau hudu, kuma na hudun ma ya zamo mai dauko hoton ciki ne sosai na na'urar 5D a lokacin da cikinta ke wata shidda wani asibitin daban.

A lokacin ne aka gano akwai yiwuwar cewa jaririn na da nakasa, amma Dakta Carvalho ya yi watsi da batun.

"Ya yi mana bayanin cewa wani lokaci ba a ganin wasu sassan fuskar jariri a idan aka yi hoton ciki," 'yar uwar iyayen Rodrigo ta shaida wa kamfanin AFP.

Bayan haihuwar Rodrigo, an shaida wa iyayensa cewa ba zai rayu ba.

Sai dai, bayan sama da mako biyu, jaririn na nan da ransa.

Rahotanni sun nuna cewa iyayen sun shigar da korafi kan Dakta Carvalho ga ofishin babban mai shigar da kara na Portugal.

Asalin hoton, Getty Images