Tarin matsaloli ne suka haddasa faduwar 'Lion Air'

Rescue

Asalin hoton, Getty Images

Matsaloli da dama ne suka haddasa faduwar jirgin sama na Lion Air, kirar Boeing 737 Max a watan Oktoban bara da ya kashe mutane 189 kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

Masu binciken hatsarin na kasar Indonesia sun gano cewa matsalolin sun shafi shi kansa kamfanin Boeing wanda ya kera jirgin da kuma kamfanin Lion Air masu jigila da jirgin da kuma matukin jirgin kansa.

Rahoton ya bayyana cewa tun da farko ya kamata a hana jirgin tashi bayan fahimtar cewa yana da matsala, kuma daya daga cikin matukin bai gama fahimtar yadda za'a shawo kan wasu matsalolin jirgin ba.

Haka ma rahoton ya gano cewa babu shafuka 31 daga littafin kula da jirgin.

Rahoton mai shafuka 353 da aka fitar da safiyar Juma'a ya nuna cewa wata na'ura da aka saya a wani shagon gyara a Florida ba'a mata gwajin da ya dace ba kafin amfani da ita.

To amma wannan wata matsala ce daya tak, a cikin jerin matsalolin da rahoton ya gano.

A hirarsa da manema labarai, daya daga cikin masu binciken Nurcahyo Utomo ya ce, binciken su ya gano cewa matsaloli tara ne suka haddasa hatsarin.

Ya kara da cewa da a ce an iya kaucewa daya daga cikin matsalolin, to da wata kila hatsarin bai faru ba.

Daya daga cikin matsalolin da suka haddasa hatsarin sun hada da matsalar lalacewar na'urar da ke hana jirgi tsayawa a lokacin da ya ke tafiya.

Bugu da kari, daya daga cikin matukan jirgin ba shi da kwarewa yadda yakamata, kamar yadda gwajin da aka yi masa a baya ya nuna.

Kuma kafin faruwar hatsarin, ya yi ta kokarin fahimtar yadda zai shawo kan matsalar, abin da ya kamata a ce tuni ya haddace a kansa.

To amma rahoton ya ce kyaftin din jirgin bai fahimtar da shi ba yadda ya kamata kafin mika masa jan ragamar jirgin, yayin da suke ta kokarin ganin jirgin ya cigaba da tafiya a sama.

Dama kafin yanzu tawagar masu binciken na Indonesia ta bayyana cewa jirgin kirar Boeing 737 Max na da matsala a na'urorinsa.