Emery ya kasa kare kansa kan Ozil

Emery da Ozil

Asalin hoton, Getty Images

Mai horar da yan wasan Arsenal Unai Emery ya ki tattauna dalilan me ya sa ya ki saka Mesut Ozil wasan Europa League da su ka yi nasara akan Vitoria Guimaraes.

Tsohon dan wasan tsakiyar Manchester City Jack Rodwell da a yanzu ba shi da yarjejeniya da wata kungiya na tattuanawa da kulob din Roma na Italiya.

Makwabtan Manchester City kuwa wato United na sha'awar dauko dan gaban Bayern Munich da Jamus Thomas Muller a watan Janairu.

Daraktan wasanni a Borussia Dortmund na Jamus Michael Zorc ya musanta jita-jitar cewa kulob din zai kawo tsohon mai horar da yan wasan Chelsea da Manchester United Jose Mourinho.

A wata mai kama da haka zai yi wuya Man U ta iya kawo mai tsaron gidan Leicester Ben Chilwell da kuma dan wasan tsakiya James Maddison a watan Janairu.

Chelsea na fatan za'a dage haramcin da aka musu na sayen yan wasa, kuyma suna sa ran kulla yarjejeniya da dan gaban Bournemouth Callum Wilson da kuma na RB Leipzig da ke Jamus Timo Werner.

A wata mai kama da haka tsohon dan wasan Manchester United Paul Scholes ya shawarci kulob din da ya kawo Mesut Ozil don warware matsalar yan gaba da kulob din ke da shi.

A cewar Scholes yakamata United ta yi amfani da damar da ta ke da ita, ganin cewa dan wasan ba ya jin dadin zama a Arsenal.

Kadan ya rage Manchester City ta kasa kawo Pep Guardiola, kasancewar ya kasa samun irin gidan da ya ke so ya zauna a Manchester.