Minista ya yi murabus kan bayar da cin hancin kankana da kaguwa

Japan's Trade Minister Isshu Sugawara speaks to the media at the parliament in Tokyo on October 25, 2019. -

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

Isshu Sugawara ya yi magana da manema labarai bayan ya sanar da murabus dinsa

Sabon ministan kasuwancin Japan ya ajiye aiki, bayan da aka zarge shi da saba dokokin zabe.

Rahotanni sun nuna cewa Isshu Sugawara ya bai wa 'yan mazabarsa a Tokyo kankana da lemo da kwan kifi.

Ana kuma zargin cewa ya bayar da kudin sadaka har dala 185 ga iyalan wani magoyin bayansa.

Dokar zabe a japan ta haramtawa 'yan siyasa aika wa da gudumuwa ga masu zaben da ke yankunansu.

Zarge-zargen sun fara bayyana ne a wata mujalla mai fitowa duk mako mai suna Shukan Bunshun, wadda ta ce sakatariyar ta bayar da kudin ne ga iyalan wani magoyin bayansa da ya rasu.

Al'ada ce a Japan a bayar da kudin sadaka ga iyalai masu alhini.

Mujallar ta buga sunayen wasu kyaututtuka da aka aika daga ofishinsa, ciki har da kwan kifi da lemo da kuma wasikun godiya da mutane suka tura masa.

Mista Sugawara ya shaida wa manema labarai ranar Juma'a cewa ko ya saba doka ko bai saba ba, ya yanke shawarar sauka daga mukaminsa.

"Ba na so matsalolina su jawo tsaiko a ayyukan majalisa," in ji Mista Sugawara.

Firai minista Shinzo Abe ya ce: "Na dauki alhakin nada shi. Ina matukar bai wa al'umar japan hakuri."