'Yan fashi na son mazauna wani kauye a Katsina su biya N2m

Katsina map
Bayanan hoto,

Jihohin Katsina da Zamfara da Sokoto da Kaduna dai na fama da ayyukan 'yan fashi, wadanda sukan kai hare-hare da sace mutane su yi garkuwa da su, baya ga fashi da makami

Al'ummar wani gari cikin jihar Katsina a Najeriya sun ce ba za su iya komawa gidajensu ba, saboda gaza biyan kudin da 'yan fashi masu satar mutane suka dora musu.

Wasu mutanen garin Dagwarwa da BBC ta zanta da su daga yankunan da suke gudun hijira sun ce, ba za su iya hada naira miliyan biyu da 'yan fashin suka nema ba, don kuwa sun baro garinsu ba tare da komai ba lokacin da aka tarwatsa su.

Jihohin Katsina da Zamfara da Sokoto da Kaduna dai na fama da ayyukan 'yan fashi, wadanda sukan kai hare-hare da sace mutane su yi garkuwa da su, baya ga fashi da makami.

Kauyen Dagwarwa na da nisan kilomita 35 daga karamar hukumar Safana, sun kuma shafe kusan wata bakwai da barin kauyen nasu bayan da 'yan fashin suka fatattake su.

'Yan fashin dai na bukatar mazauna kauyen su biya su naira miliyan biyu ne kudin wata bindigarsu da ta salwanta yayin arangamarsu da jami'an tsaro.

Mazauna kauyen sun cewa BBC kimanin mako biyu da suka gabata ne 'yan fashin suka gayyace su domin yin sulhu inda suka bukaci su biya wannan kudin kafin su bari su koma mahaifarsu.

Wani da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce: "Asabar can ta sama da ta wuce ne suka kira mu suka ce mu hadu a garin Dagwarwan misalin 12, bayan mun isa kuma sai suka ce mu karasa can cikin daji Bakin Lamba. Ba mu wakilta kowa ba mu da kanmu manyan garin muka je.

"Da zuwanmu wajen sai muka tarar da mutanen da makamai bindiga ta kai 20, abin sai ya fadar min da gaba ma.

"Tun 12 muke wajen ba su waiwaye mu ba sai wuraren biyar na yamma sannan suka ware dattijai biyar cikinmu da mutum biyar daga cikinsu suka koma kauyen suka yi shawara suka ce za a ba su kudi naira miliyan biyar.

"Daga nan wajen aka roki alfarma daga haka har aka sauko zuwa miliyan biyu," in ji mutumin.

Shi ma wani mazaunin garin daban ya ce "a yanzu haka duk cikinmu babu mai dubu 100 wasu ma sai sun yi bara suke samun abin da za su ci."

Asalin hoton, Masari Facebook

Bayanan hoto,

A watan Agusta ne gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya ce zai shiga daji domin sasantawa da masu kai wa jama'ar jiharsa hare-hare

Sai dai duk da kokarin shiga tsakani da gwamnatin karamar hukumarsu ta yi abin ya ci tura.

"Maganar a ce a ba da kudin fansa don mutane su samu damar zama a wajen da ya zam nasu ne ba ta taso ba. Sannan idan ka tura jami'in tsaro me zai yo a wajen? Ai babu mutane a garin ma balle ka tura jami'an tsaro," in ji kantoman karamar hukumar Safana.

Al'ummar Dagwarwa dai manoma ne da adadinsu ya haura mutum 3,000, kafin 'yan fashin daji su fafare su cikin watan azumi.

Yanzu haka suna gudun hijira a wurare daban-daban da suka hada da jihohin Neja da Kano da Bauchi da Gombe har da Jamhuriyar Nijar.