Abu Bakr al-Baghdadi: Ko mutuwar shugaban IS nasara ce ga Trump?

Baghdadi addressing crowd in Mosul, 2014

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Baghdadi ya sanar da kirkirar "daula" daga Mosul a shekarar 2014

Mutuwar jagoran kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi ta zama nasara ga shugaban Amurka Donald Trump, a yayin da yake fuskantar kakkausar suka kan matakinsa na janye dakarun Amurka daga arewa maso yammacin Syria - da kuma kokarin kalubalantar binciken tsige shi da jam'iyyar Democrats ke yi.

Mista Trump ya ce shugaban IS din ya hallaka kansa ne a yayin da sojojin Amurka suka kai hari arewa maso yammacin Syria.

Da yake magana daga Fadar White House, Mista Trump ya ce Abu Bakr al-Baghdadi ya sanya jigidar bam ne bayan ya tsere cikin wata hanya ta karkashin kasa, inda karnukan sojojin Amurka suke bin sa.

Kwana guda bayan mutuwar jagoran kungiyar IS din, rahotanni na cewa an sake halaka wani jigo a kungiyar.

Wani shugaban Kurdawa ya ce Amurka ta halaka Abu Hassan Al Muhajir, kakakin kungiyar IS kuma wanda ake tunanin zai gaji al-Baghdadi.

Kawo yanzu Amurka ba ta tabbatar da mutuwarsa ba amma kafafen yada labaran kasar na cewa hare-hare ta sama da aka kai sun rutsa da Al Muhajir a lokacin da yake bulaguro zuwa arewacin Syria.

Amma kawayen Amurka sun ce kisan al-Baghdadi ba yana nufin yaki da kungiyar ta IS ya zo karshe ba ne.

A shekarar 2014 ne aka fara sanin al-Baghdadiyayin da ya sanar da kirkirar "daular musulunci" a yankunan Iraki da Syria.

IS ta kai hare-hare masu muni da suka jawo mutuwar dubban mutane.

Kungiyar ta dinga aiwatar da jagoranci ta hanyar kisan gilla a yankunan da ke karkashin ikonta kuma su ne ke da hannu wajen kai wasu manyan hare-hare da suka faru a duniya.

Duk da cewa Amurka ta ayyana "daular" a matsayin wacce aka yi nasara a kanta a wannan shekarar, mayakin IS sun ci gaba da zama masu karfi a yankin da ma wasu wuraren.

A wata sanarwa da Shugaba Trump bai saba fitar da irinta a ranar Lahadi ba, Mista Trump din ya bayyana samamen da aka kai da dare na kashe al-Baghadadi a matsayin wani abu na daban, inda ya ce al-al-Baghdadi ya fada ciikin tarkon mutuwarsa ''yana ihu da kuka,'' yayin da karnukan sojoji ke binsa.

al-Baghdadi ya kashe kansa da yaransa uku bayan ya tayar da bam din da ke jikinsa inji Mista Trump wanda ya ja hanyar karkashin kasar da ya bi ta fashe. Babu wani sojan Amurka da ya rasa ransa sakamakon tashin bam din sai dai daya daga cikin karnukan sojojin Amurkar ya raunata matuka.

Shugaban kasar ya bayyana cewa fashewar bam din ya tarwatsa sassan jikin al-Baghdadi, kuma wani gwajin kwayoyin halitta da aka gudanar da wurin da lamarin ya faru ya tabbatar da cewa lallai shi ne ya mutu.

Sojoji na musamman da suka kai sumamen sun shafe kusan sa'o'i biyu a wurin suna tattara bayanai kuma sun samu bayanai da abubuwa matuka inji shugaban.

A ranar Lahadi, mayakan Kurdawa na SDF sun bayyana cewa mai magana da yawun Kungiyar IS Abu al-Hassan al-Muhajir wanda na hannun daman al-Baghdadi ne an kashe shi a wani harin hadin gwiwa da Amurkar ta kai kusa da garin Jarablus na Syria.

Abubuwan da suka fito fili game da kashe al-Baghdadi

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kauyen da aka kashe al-Baghadadi wato Barisha da ke Idlib wanda yake kusa da iyakar Turkiyya, gari ne da ke da nisa da inda ake tunanin ya boye a kusa da iyakar Syria da Iraki.

Sassa da dama na Idlib na karkashin kungiyar masu ikirarin jihadi da ke adawa da IS amma duk da haka ana zargin kungiyoyin da ke adawar da kare wasu mayakan IS.

An yi makonni kusan uku ana sa ido kan al-Baghdadi kafin a kai wannan samamen.

Sojojin da ba a bayyana adadinsu bane suka kai hari a gidan tare da jirage masu saukar ungulu takwas inji Mista Trump. Jagororin kai samamen sun yi kokari sun sauka gidan inda suka guje wa kofar shiga ta gaba sakamakon ana zargin akwai wani tarko jikinta.

''Mutum ne mara lafiya kuma mara mutunci,'' inji Mista Trump. ''Ya mutu tamkar wani kare, ya mutu tamkar matsoraci.''

Mai bai wa Majalisar Dinkin Duniya shawara kan harkokin tsaro Robert O'Brien ya bayyana cewa kamata yayi a yi wa gawar al-Baghdadi yadda aka yi wa irin ta Shugabannin al-Qaeda na baya da suka mutu irin su Osama bin Laden, wato a zubar da ita cikin teku.

An kashe masu tsaron al-Baghadadi da dama kuma akwai da damansu da aka kama, inji Mista Trump.

Wasu daga cikin wadanda aka kashe sun hada da matan al-Baghdadi biyu wadanda aka gansu dauke da jigadar bama-bamai wadanda basu fashe ba.

An dauke yara kusan 11 da ba a kashe a gidan ba.

Nasarar Trump ta fannin dangantaka da kasashe

Dalilin da yasa aka kashe Abu Bakr al-Baghdadii ya fito fili. Cire shugaba mai tsauri da jarumtaka a filin yaki tabbas zai iya saka dakarun kawance su yi kokarin tarwatsa Kungiyar IS.

Baghadi na da nisa da wani gida a Amurka, sai dai an san IS matuka tun bayan kashe mutanen da ta fara yi wanda hakan ya jawo aka santa a 2014.

Mutuwarsa ta bar wa Mista Trump wani tarihi da zai yi amfani da shi ko kuma tinkaho kan cewa gwamnatinsa ce ta kawo karshen mayakan IS.

Duk da cewa gaskiya ne Amurka ta fi mayar da hankali da dangantakarta tsakaninta da kasashe a lokacin yaki, duk matsalolin da Trump ke fuskanta sun samo asali ne daga abubuwan da ke faruwa a ketaren kasar - ko kan batun Syria ko kuma kan batun tsige shi da ake yi.

Yanzu shugaban na da abin da zai iya tinkaho da shi ta bangaren dangantakarsa da kasashen ketare. Hakan ba zai kawo karshen duka matsalolinsa a siyasance ba, amma matsalolin za su ragu.

Ya duniya ta dauki mutuwar al-Baghdadi?

Shugabanni a fadin duniya sun mayar da martani dangane da mutuwar Abu Bakr al-Baghdadi inda da dama daga cikinsu ke cewa za a ci gaba da yaki da kungiyar IS.

Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana mutuwar al-Baghdadii a matsayin ''wani muhimmin abu a fadan da ake yi da ta'addanci amma fadan da ake yi da IS bai kare ba.''

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana wannan ci gaba a matsayin wata ''babbar nasara'' da aka samu kan IS amma ''za a ci gaba da yakarsu har sai an tarwatsa kungiyar 'yan ta'addan.''