Kungiyar Liverpool ta yi nasara a kotu

A

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta samu nasara a kotu kan wata shari'a da ta shafi daukar dawainiyar kungiyar a wata yarjejeniya da wani kamfani na kasar Amurka mai suna New Balance.

An kai karar kungiyar saboda kin cika sharudda a yarjejeniyar da ta kai fan miliyan 40 a kowacce shekara.

A karkashen yarjejeniyar, kamfanin mai yin takalman kwallon nada damar sabunta yarjejeniyarsa da Liverpool, idan har ya ba da kudi daidai da wani kamfanin da suke goggayya domin daukar dawainiyar Liverpool din.

Sai dai kungiyar Liverpool ta ce kamfanin New Balance ya kasa gogayya da kamfanin Nike kan yarjejeniyar shekaru biyar da ta kai dala miliyan 30 a duk shekara.

A lokacin yanke hukuncin, alkalin ya ce kungiyar Liverpool ba ta saba ka'ida ba.