Saudiyya ta shiga jerin kasashe 10 da ake son zuba jari

Saudi Arabia

Asalin hoton, Gazette

Sauye-sauyen da kasar Saudiyya ta kaddamar dangane da samar da yanayin kasuwanci da zuba jari a 2018, al'amarin da ya sa Saudiyyar shiga jerin kasashe 10 a duniya da suka inganta yanayin kasuwanci, kamar yadda wani rahoton Bankin Duniya kan samar da yanayin kasuwanci na 2020 ya fitar.

"Sauye-sauyen da Saudiyya ta samar na nuna irin jajircewarta na ganin ta cimma burinta na kasancewar babba a harkar tattalin arziki a duniya a 2020," in ji Issam Abousleiman, jami'i a Bankin Duniya .

Rahoton ya zayyana sauye-sauyen da Saudiyyar ta zartar guda takwas da suka inganta harkar kasuwanci a kasar.

• An saukaka yin kasuwanci kasancewar yadda Saudiyya ta mayar da tsarin yin rijista na bai daya. Sannan kuma masarautar ta bai wa mata masu aure damar yin rijistar katin dan kasa ba tare da wasu sharudda ba.

• An saukaka samun lasisin yin gine-gine ta hanyar intanet.

• Samar da wutar lantarki.

• Samar da kudaden rance domin fara kasuwanci.

• Bai wa kananan masu zuba jari kariya.

• Inganta shige da ficen kayayyaki ta hanyar inganta tashar jiragen ruwa ta Jeddah.

• Inganta tsarin kwangila ta hanyar wallafa kwantaragi.

• Taimaka wa masu jarin da suka karye biyan bashin da ake bin su.