'Yan Zimbabwe na yi wa Amurka da zanga-zanga

Protesters

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Government supporters chanted slogans in Harare, in one of the country-wide marches

Dubban 'yan kasar Zimbabwe suka shiga zanga-zangar da gwamnatin kasar ke mara wa baya domin nuna kin jinin jerin takunkuman da Amurka da Tarayyar Turai suka kakaba wa kasar.

To sai dai Amurka da Tarayyar Turai sun ce sun sanya wa dai-daikuwar mutane da kamfanoni jerin takunkumin ne a saboda haka ba shi da tasiri a kan gwamnati.

Gwamantin kasar dai ta ayyana ranar Juma'a ranar hutu, inda kuma gwamnatin ta dauki nauyin motocin daukar jama'a sannan kuma shugaba Emerson Mnangagwa ya yi jawabi a filin wasa na kasar.

Shugaba Mnangagwa ya ce "mun sani sarai cewa jerin takunkumin ba su dace ba," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya shaida wa dandazon masu zanga-zanga.

Ya kara da cewa "Tasirin takunkumin a kan rayuwarmu ta yau da kullum ba zai misaltu ba sannan muna wahala."

Masu zanga-zangar sun sanya rigunan da aka rubuta taken "#SanctionsMustGo" da ke neman a cire takunkuman tare da daga kwalayen da ke nuna rashin imanin takunkuman ga jama'a.

Wadanda suka gabatar da jawabai yayin taron, sun cewa takunkuman ne ke da alhakin yanayin kunci da Zimbabwe take ci da kamar matsalar rashin wuta da karancin ruwa.

Ofishin jakadancin Amurka a Zimbabwe ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa tabarbarewar tattalin arzikin kasar ya taallaka ne ga irin gazawar tsare-tsaren gwamnatin na tattalin arziki.

A yanzu haka dai Amurka ta kakaba takunkumin hana shiga Amurka da yin amfani da kudade ga mutum 85 'yan kasar ta Zimbabwehe da suka hada da shugaba Mnangagwa da kuma wasu kamfanoni 56.

Har wa yau, Amurkar dai ta kakaba haramta shigar da makamai Zimbabwe.

Ita ma Tarayyar Turai ta saka wa wasu mutane da ke cikin gwamnatin Zimbabwe ko kuma masu alaka da ita.