An ceto sama da mutum 100 daga gidan mari a Kwara

BBC

'Yan sanda a Najeriya sun kai samame a wani gidan mari da ke jihar Kwara inda suka ce sun ceto kusan mutane 108.

Wadanda aka ceton sun hada da maza da mata da kuma kananan yara wadanda aka gansu daure cikin sarkoki.

Wannan ne karo na shida da ake kai samame a irin wadannan gidaje a wannan watan bayan zarge-zargen da ake yi na cewa ana azabtar da mazauna gidajen da sunan gyaran tarbiyya.

Bayan da aka fara kai irin wannan samame, Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya jinjina wa rundunar 'yan sandan kasar kan irin wannan kokarin da kuma basu umarnin ci gaba da kai samame irin wadannan wurare.

A wannan samamen da aka kai a Kwara, 'yan sandan sun gano mazauna wannan gida cikin wani mummunan hali. rahotanni sun shaida cewa an kama mai gidan marin da aka kai samamen.

A lokuta da dama, iyaye na kai 'ya'yansu wadanda suka kangare ko kuma suke ta'ammali da miyagun kwayoyi irin wadannan gidaje domin gyara tarbiyyarsu amma a wasu lokutan sai a ci zarafinsu.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kwara Egbetokun Kayode ya shaida wa BBC cewa wadanda aka ceton za a yi kokarin hada su da iyalansu.

Rabiu Umar wanda aka taba tsarewa a wani gidan marin da aka kai samame a kwanakin baya ya shaida wa BBC cewa an ci mutuncinsa kamar ''dabba.''