Kotu ta aika Abdulrasheed Maina gidan kaso

bbc
Bayanan hoto,

Abdulrasheed Maina zai sake bayyana a gaban kuliya ranar 30 ga Okotoba

Alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Okon Aban ya aike da tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul, Abdurrasheed Maina bayan da bukatar da lauyoyinsa suka gabatar ta neman beli ta gaza gamsar da kotun.

Lauyoyin gwamnati ne dai suka nemi kotun ta yi watsi da bukatar belin kasancewar Abdurrasheed Maina ya nemi belin ne tun ma kafin zaman kotun.

Yanzu haka an dage bukatar neman belin har sai zuwa ranar 30 ga watan Oktoban 2019, inda wanda ake karar zai sake bayyana.

Shi kuwa Faisal Abdulrasheed Maina wanda da ne ga Maina zai ci gaba da zama a hannun 'yan sanda har zuwa lokacin da zai sake gurfana a gaban kuliya ranar 6 ga watan Nuwamban 2019.

Hukumar EFCC ce dai ta gurfanar da Maina da dan nasa a gaban kuliya ranar Juma'a bisa tuhuma 12, inda shi kuma dan nasa ake tuhumar sa da laifuka uku.

A ranar Talatar da ta gabata ne kuma alkalin wata babbar kotu a Abuja, mai shari'a, Folashade Giwa Ogunbanjo ya bayar da umarnin cewa gwamnatin tarayya ta karbe kadarori guda 23 mallakar tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho a Najeriya garambawul, Abdulrasheed Maina.

Mai shari'a Ogunbanjo ya bayyana kwace kadarori mallakar Maina ne sakamakon wata kara da hukumar EFCC ta shigar, inda ta nemi da a mallaka wa gwamnati kadarorinsa na dan wani lokaci har zuwa lokacin da za ta kammala bincike.

Kadarorin mallakin Maina da kwacewar ta shafa sun hada da wadanda ke a Abuja da Kaduna da Sokoto da Borno.

Bayanan hoto,

EFCC ta ce ta kama Faisal Abdulrasheed Maina ne tare da mahaifinsa a otal, inda ya tasar wa jami'anta da bindiga a hannunsa