Soja ya buda wa 'yan uwansa sojoji wuta a Rasha

map

Wani jami'in soji a Rasha ya harbe abokan aikinsa takwas tare da jikkata wasu biyu a sansaninsu da ke gabashin kasar.

Da alamu Ramil Shamsutdinov, wanda tuni aka tsare shi yana da tabin hankali kamar yadda jami'ai suka bayyana.

Al'amarin ya faru ne ranar Juma'a da daddare a sansanin da ke kauyen Gorny wanda ba shi da nisa daga birnin Chita.

Tuni dai aka kaddamar da bincike kan wannan ibtila'in da ya faru.

Abinda aka sani game da kisan.

Al'amarin ya faru da karfe 11:15 agogon GMT a cewar kwamitin bincike da Rasha ta kafa.

Ma'aikatar tsaron kasar tun farko ta ce jami'in ya harba bindigar ne a lokacin da sojojin ke sauya aiki.

Mista Shamsutdinov ya kashe ma'aikata biyu da wasu 'yan uwansa sojoji shida.

Mataimakin ministan tsaro, Andrey Kartapolov shi zai jagoranci hukumar da za ta gudanar da bincike kan al'amarin.

A tsarin Rasha, aikin soji wajibi ne ga maza 'yan shekara 18 zuwa 27 inda suke shafe tsawon shekara guda suna bada gudummawa sannan kuma daga nan idan suna sha'awa su nemi kwantiragin zarcewa zuwa rundunar soji.

A baya, kungiyoyin kare hakkin bil adama sun sha sukar gwamnatin Rasha da cin zarafin sojojinta, sai dai a baya-bayan nan, kasar ta yi ikirarin zamanantar da rundunar sojinta.