Kaduna: An sako daliban makarantar Engravers College

Malam Nasir El Rufai

Asalin hoton, @elrufai

Bayanan hoto,

'Yan bindiga sun yi wa Kaduna kaka-gida

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kadunan Najeriya ta tabbatar da sakin dalibai mata da aka sace a jihar 'yan makarantar Engravers College a farkon watan Oktoban nan.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar DSP Yakubu ya tabbatar wa da BBC sakin nasu, inda ya ce an ceto dukkanin daliban shida da malaminsu guda daya da kuma ma'aikaciya daya.

A ranar 2 ga watan Oktoba ne wasu 'yan bindiga suka yi awon gaba da dalibai mata shida daga makarantar Engravers College tare da malamai biyu, wadda ke garin Kakau me nisan kilomita 10 daga kamfanin mai na NNPC na Kaduna.

Shi ma Samuel Aruwn, Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida na jihar, ya tabbatar da faruwar al'amarin kuma ya ce tuni aka hada su da iyalansu.

"Abu mafi mahimmanci shi ne cewa an ceto su kuma tuni sun isa wurin iyayensu," in ji Samuel Aruwan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Babu bayani kan ko an biya kudin fansa

Da wakilin BBC ya tambaye shi karin bayani game da yadda aka gano su, sai ya ce ba zai iya yin magana kan harkokin tsaro ba. Kazalika babu bayani kan ko an biya kudin fansa.

Sai dai DSP Yakubu Sabo ya ce 'yan bindigar ne suka saki yaran a daji bayan sun yi arba da 'yan sanda.

"Da 'yan sanda suka bi su ba su iya ganin inda suka yi ba, sai suka debi yaran zuwa ga iyayensu," in ji shi.

Ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin kama wadanda ke da hannu wajen aikata wannan laifi.

Jihar Kaduna na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro iri-iri a baya-bayan, inda 'yan bindiga ke yin garkuwa tare da kashe mutane babu gaira babu dalili.

A ranar Litinin da ta gabata 'yan sanda a jihar suka ba da sanarwar nasarar kubutar da babban jami'in dan sandan nan da aka sace, ACP I. Musa, mai lakabin Rambo, a kan hanyar Kaduna zuwa Jos.