IS: Amurka 'ta halaka Abu Bakr al-Baghdadi shugaban kungiyar IS'

Shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An sha ruwaito mutuwar Abu Bakr al-Baghdadi a baya

Amurka ta halaka shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi, wanda yake gudun hijira, a wani hari da sojojinta suka kai a arewacin kasar Syria, a cewar Shugaba Donald Trump.

Da yake magana daga cikin fadar White House, Trump ya ce al-Baghdadi ya tarwatsa kansa ne da rigar bam da ke jikinsa bayan dakaru na musamman sun ritsa shi a karshen wata hanyar karkashin kasa.

Al-Baghdadi ya shahara a duniya a shekarar 2014 bayan ya ayyana wasu yankuna na Iraki da Syria a matsayin "daular Musulunci".

A wani jawabi da ba a saba ganin irinsa ba, Mista Trump ya ce Baghdadi ya mutu ne bayan ya tsere zuwa wata hanya maras bullewa, "yana ihu tare da neman dauki" yayin da karnuka ke biye da shi.

Al-Baghdadi yana tare da 'ya'yansa guda uku, in ji Trump, sannan ya tayar da bam din da ke jikinsa, abin da ya yi sanadiyyar kashe su duka.

Ya kara da cewa bam din ya yi watsa-watsa da jikinsa amma gwajin kwayar halitta ya tabbatar da cewa shi gawarsa ce.

"Dan daban da ya yi kokarin tilasta wa mutane ya kare lokutan karshe na rayuwarsa ne cikin matsanancin tashin hankali da kuma tsoron sojojin Amurka," Mista Trump ya bayyana.

Kungiyar IS ta haddasa kashe-kashe da barna iri-iri, abin da ya jawo mutuwar dubban mutane.

Masu ikirarin jihadin sun saka dokoki masu tsaurin gaske a kan kusan mutum miliyan takwas da ke karkashin ikonsu sannan suka kai hare-hare da dama a fadin duniya.

A farkon wannan shekarar ne Amurka ta ce ta rusa"daular".

Tun farko dai Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Wani babban lamari ya faru yanzun nan!"

A baya dai an sha bayar da rahotannin mutuwar shugaban kungiyar ta IS.

Wani kwamandan mayakan Kurdawa a karkashin kungiyar Syrian Democratic Forces mai suna Mazloum Abdi ya ce "wani hari mai cike da tarihi da nasara" na hadin gwiwa da sojojin Amurka ya haifar da sakamako mai kyau.