Shugaban kasar Chile ya bi umarnin masu zanga-zanga

Shugaban kasar Chile Sebastian Piñera

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mista Piñera ya yi alkawarin kawo karshen rashin daidaito tsakanin 'yan kasarsa

Shugaban kasar Chile Sebastian Piñera ya kori dukkanin ministocin gwamnatinsa domin kafa sabuwar majalisar zartarwa tare da aiwatar da wasu gyare-gyare kamar yadda masu zanga-zanga suka bukata.

"Na bai wa dukkanin ministocina wa'adi domin aiwatar da bukatun da aka gabatar mani," in ji shi.

Har yanzu dai ba a san wane irin tsari zai bi ba na kafa sabuwar majalisar zartarwar tasa.

Sama da mutum miliyan daya ne suka hau tituna a ranar Juma'a domin yin zanga-zangar lumana tare da kiran da a kawo gyara game da yadda gwamnati ke amfanar 'yan kasa a babban birnin kasar Santiago.

Mista Piñera ya ce ya samu labarin bukatun nasu ne a gari.

"Abubuwa a bayyane suke karara," ya fada,. Ya kara da cewa: "Chile ta sauya daga yadda aka san ta mako daya da ya gabata."

Shugaban kuma ya bayyana cewa dokar ta-bacin da aka saka a wasu birane a makon jiya ita ma an dage ta.

'Yan adawa a kasar da ma sun yi ta kiraye-kirayen da a janye dokar ta-bacin.

Me ya jawo zanga-zangar?

Zangar-zangar ta samo asali ne daga karin kudin shiga jirgin kasa da gwamnati ta yi, wanda tuni ta soke, amma sai ta rikide zuwa bukatar neman gyara game da tsadar rayuwa da kuma rashin daidaito tsakanin 'yan kasa.

An samu sace-sace da fasa shagunan kasuwanci yayin zanga-zangar. Sama da mutum 7,000 aka kama.

Sojojin kasar ne suka karbi aikin tsaron titunan birnin Santiago, wanda ke kan dokar ta-baci, tare da dubban 'yan sanda a hannu guda.