Mutumin da ya 'mutu' a Kano an gano shi a Bauchi bayan shekara 30

WhatsApp ya taimaka wajen gano cewa ashe yana raye

Asalin hoton, Yakubu Musa

Bayanan hoto,

WhatsApp ya taimaka wajen gano cewa ashe yana raye

Iyalan mutumin da 'yan uwansa suka dade da rungumar kaddarar mutuwarsa bayan samun labarin rasuwarsa shekaru da dama sun sake yin tozali da shi.

Shekaru 30 da suka gabata dangin Aminu Baita, suka samu labarin cewa ya fada kogi ya mutu.

Amma a wani lamari da ya zo da mamaki, sai ga shi an samu Aminu Baita a jihar Bauchi ta sanadiyar yada wata sanarwar cigiyar wani a kafar WhatsApp wanda ya bata.

Nasidi Musa, dan uwa ne ga Aminu Baita kuma ya ce al'amarin ya samo asali ne "bayan karanta wani sakon cigiyar batan wani Audu Musa Gagarawa a shafin sada zumunta na Whatsapp dauke da hotonsa."

"Dan uwan sirikata ce da shi ma ya yi batan dabo ba tare da an san inda yake ba," in ji Nasidi Musa.

Ya bayyana cewa sirikar tasa ta bukaci ya je karamar hukumar Toro a jihar Bauchi inda aka ce shi wanda ake neman 'yan uwansa ya ke. Bayan ya je ne kuma ya hadu da jami'an karamar hukumar da suka kai shi har wajen mutumin amma kuma ya kasa gane ko shi ne ainihin mutumin da sirikarsa ta ce shi ne dan uwanta.

"Na kira ita sirikar tawa domin ta sanar da ni wata alama da za a iya gano dan uwan nata tun da ba mu iya tantance ko shi ne ko kuma ba shi ba ne."

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ya kara da cewa ita sirikar ta bukaci su duba gefen fuskarsa za su ga wani katon tabo wanda ya same shi sanadiyyar wani hadarin babur da ya gamu da shi sai dai Nasidin ya ce labari ya sauya ne bayan da ya gano cewa wanda sirikarsa ta ke tunanin dan uwanta ne, shi ne dan uwansu da suka yi zaton ya mutu har suka yi masa jana'iza ba tare da ganin gawarsa ba shekara 30 da suka gabata.

''Bayan na gano cewa mutumin shi ne dan uwanmu, Aminu Baita, na sake tuntubar sauran 'yan uwa kan halin da ake ciki inda kuma nan da nan aka dawo da shi jihar Jigawa kuma tuni suka kai shi asibiti," in ji shi

A cewarsa, Aminu Baita wanda ake tunanin ya mutu, mutum daya kawai ya iya gane wa wato yar uwarsa mai suna Hajiya Asabe.

Dan uwan ya kuma ce tsawon lokacin da ya shafe a Toro, yana wani wajen Bawan Allah wanda ya ke dawainiya da dan uwan nasu.

Nasidi ya nuna farin cikinsa dangane da wannan baiwa inda ya ce za su ci gaba da nema ma sa magani.

Abinda aka sani game da Aminu Baita

Kafin wannan lamari ya faru ga Aminu Baita, 'yan uwansa sun ce jami'in kiwon lafiya ne mai kula da jinyar marasa lafiya kuma yana aiki ne a ma'aikatar lafiya ta jihar Kano kuma yana da aure.

Sun ce Baita ya fara nuna alamar yana da matsalar rashin lafiyar kwakwalwa wanda likitoci suka tabbatar abin da suka ce shi ne sanadiyyar rasa aikinsa sannan suka rabu da mai dakinsa.

Bayan haka ne 'yan uwansa suka kai shi cibiyar kula da masu rashin lafiyar kwakwalwa a karamar hukumar Dambatta inda a nan ne aka ce Aminu Baita ya mutu bayan sanar da su cewa Aminu ya faki ido ya fice daga wajen da ake kula da su inda kuma kai tsaye ya nufi wani kogi, a nan ne kuma ya nutse har rai ya yi halinsa.

Yakubu Musa, dan uwa ga Aminu Baita ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce tun bayan da suka samu rahoton ya nutse a kogi ne suka yi ta kokarin ganin an zakulo gawarsa amma kuma hakan bai samu ba.

Hakan ta sa suka rungumi kaddarar cewa dan uwansu ya mutu.