Mutanen Borno dubu 140 suka yi gudun hijira a 2019 - MDD

'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum 140,000 rikicin Boko Haram a jihar Borno ya tilastawa yin gudun hijira a shekarar 2019 kawai.

Sakatare Janar na hukumar kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Mark Lowcock, wanda ya kai ziyara jihar Borno ya ce Ya ce sabbin hare-haren Boko Haram ne suka tilastawa mutanen gudun hijira.

Ya ce sama da mutum miliyan uku ke fuskantar barazanar karancin abinci sakamakon hare-haren da suka hanawa manoma yin shuka.

Sama da mutum miliyan bakwai ke bukatar agaji a jihohin arewa maso gabashi Borno da Adamawa da Yobe, a cewar Mista Mark Lowcock

Ya kara da cewa shekaru 10 na rikicin Boko Haram ya tagayyara al'ummar yankin.

Gwamnatin Najeriya dai ta dade tana ikirarin cewa ta karya lagon Boko Haram, amma har yanzu mayakan kungiyar na kai hare-hare kan sansanonin soji da kuma fararen hula.