Buhari zai halarci taron kasuwanci a Saudiyya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai kai ziyara Riyadh babban birnin Saudiyya domin halartar taron zuba jari karo na uku da kasar ke jagoranta.

Taron na yini uku mai taken "Me nene mataki na gaba ga kasuwancin duniya", zai kuma mayar da hankali ne kan yadda za a inganta fasaha domin amfanin duniya a nan gaba.

Yarima mai jiran gado Muhammad Bn Salman Abdulaziz kuma shugaban hukumar samar da ci gaba da bunkasa tattalin arzikin Saudiyya ne zai jagoranci taron.

Sanarwar da mai ba shugaban shawara kan yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar ya ce, Shugaba Buhari dai zai yi amfani da wannan dama wajen yin jawabi kan irin tarin damarmakin da Najeriya ta ke da su ga ma su saka jari..

Sannan zai yi bayyana yadda gwamnatinsa ta samar da tsare-tsaren inganta kasuwanci domin janyo hankalinsu.

Bayanai dai sun ce yawan kudaden shiga na Najeriya sun karu daga dala biliyan 12 a farkon rubu'in shekarar 2018 zuwa dala biliyan 14 a watanni ukun farko na shekarar 2019.

Garba Shehu ya ce tawagar Najeriya za ta nemi masu saka jari su zuba kudadensu a bangarorin mai da iskar gas musamman shimfida bututun iskar gas mai nisan kilomita 614 da zai tashi daga Ajaokuta ya bi ta Kaduna ya kuma zarce Kano.

Jami'an Najeriyar za kuma su yi amfani da taron wajen fadada tattaunawa kan sha'awar kamfanin man kasar Saudiyya, Aramco na bunkasawa tare da farfado da matatun man kasar.

Taron wani bigire ne ga masu zuba jari da gwamnatoci da masu fasaha su tafka muhawara da nufin gyara makomar zuba jari a fadin duniya.

Sama da wakilai 4,000 ne daga kasashe sama da 90 za su halarci taron da zai kuma gudanar da tarukan karawa juna sani kan makaloli da dama da makamashi da sauyin yanayi da lafiya da abinci da tafiye-tafiye da kuma harkokin matasa.

Bayan taron kuma, shugaba Buhari zai je birnin Makkah tare da wasu masu bashi shawara domin gudanar da Umrah daga nan kuma su koma Abuja, babban birnin kasar