Buhari da Atiku: Kotun koli ta sanar da ranar Shari'a

Buhari da Atiku

Asalin hoton, @others

Kotun Kolin Najeriya ta tsayar da ranar fara sauraren karar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya shigar, inda yake kalubalantar zaben shugaba Muhammadu Buhari na APC.

Jam'iyyar PDP ta daukaka kara ne kotun koli bayan ta yi watsi da hukuncin 11 ga watan Satumba da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta tabbatar da zaben Buhari a matsayin shugaban kasa.

Babbar jam'iyyar adawar ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, cewa za a fara sauraren daukaka kararsu ne ranar Laraba 30 ga watan Oktoba.

PDP da dan takararta Atiku Abubakar sun ce akwai kuskure a hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben ta yadda kotun ta kasa gamsuwa da hujjojin da ta gabatar cewa Buhari bai cancanci tsayawa takarar ba, kuma ba shi ya samu mafi yawan kuri'u ba.

Jam'iyyar APC mai mulki a nata bangaren ta bukaci kotun koli ta yi tunani kan wasu bayanai da hujjoji da PDP ta gabatar da kotun farko.

Tun da farko APC ta ce a shirye ta ke ta kalubalanci dan takarar na jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar a Kotu.

Tsawon lokacin da za a dauka a shari'ar

Bangarorin biyu suna da adadin kwanakin da za su dauka domin shigar da dukkanin takardun daukaka kara da kuma mayar da martani.

Barrista Ali Jamil ya ce karar zabe daga karamar kotu zuwa kotun koli tana daukar kwanaki 180, wato wata shida. Wata uku a kotun sauraren karararrkin zabe sai wata biyu a kotun daukaka kara.

Amma tsawon kwanaki 30 ne za a dauka a kotun koli.

Idan an shigar da takardu alkalai za su zauna su diba bayan bangarorin biyu sun yarda da bayanan da suka gabatar.

A kotun koli ba batun gabatar da shaidu, sai dai a tattara takardun karamar kotu a kai zuwa kotun koli.

PDP da ta daukaka kara za ta fadi hujjojinta na sukar hukuncin da kotun farko ta yanke na kuskure ko gazawa amma ba batun gabatar da shaida.

Kotun koli kuma za ta diba ta yi nazari kan matakin da za ta dauka kafin tsayar da ranar zartar da hukunci.