Allah Ya yi wa Mai-dakin Sir Abubakar Tafawa Balewa rasuwa

Hajiya Jummai rasu tana da shekara 90 a duniya
Bayanan hoto,

Hajiya Jummai rasu tana da shekara 90 a duniya

Allah ya yi wa mai-dakin Firaministan Najeriya Sir Abubakar Tafawa Balewa rasuwa, matarsa da ta rage a duniya cikin matansa hudu.

Hajiya Jummai ta rasu ne a ranar Lahadi da yamma a birnin Lagos kudancin Najeriya, kamar yadda daya daga cikin 'ya'yan Marigayi Firaminista Tafawa Balewa ya tabbatar wa BBC.

Umar Tafawa Balewa ya ce a ranar Litinin za a yi ma ta sallar jana'iza a masallacin fadar mai martaba Sarkin Bauchi.

"Babban hafsan sojin saman Najeriya ya bayar da jirgi da za a dauko gawarta daga Lagos a ranar Litinin,"

"Cikin matan mahaifinmu hudu ita kadai ce ta rage, kuma yanzu Allah ya dauki ranta."

"Rasuwarta babban rashi ne domin mahaifiya ce, yanzu irinsu da suka rage sun kare," in ji shi.

Hajiya Jummai ta rasu ne tana da shekara 90 a duniya.

A shekarar 2009 matan marigayi Sir Tafawa Balewa biyu suka rasu inda Hajiya Inne uwar gidansa ta rasu a watan Disamba, yayin da kuma Hajiya Umma ta rasu a watan Fabrariu.

Umar Tafawa Balewa ya ce Shekara 10 yanzu tsakaninsu da rasuwar Hajiya Jummai - "Hajiya Laraba matarsa ta uku ce ta fara rasuwa da dadewa."

Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa ne Firaministan Najeriya na farko bayan da kasar ta samu 'yancin kai a 1960.

A ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966 aka yi juyin mulkin farko a Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyar kisan Firaministan kasar Sir Abubakar Tafawa Balewa.