Stalkerware: Manhajar da ke taya ma'aurata leken asirin juna

  • Daga Joe Tidy
  • Cyber-security reporter
Phone graphic of data moving to victim's phone.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu amfani da manhajar Stalkerware na iya ganin sakon kar ta kwana da na email da kuma samun damar amfani da kamarar wayar mutane

Amy ta ce lamarin ya dauko asali ne lokacin da mijinta ya san wasu abubuwanta na sirri da suka shafi kawayenta.

"Ya kan ya da magana idan muna tattaunawa, kamar magana kan abin da ya shafi jaririyar Sarah. Wato abubuwan ma da ba su shafe shi ba, kuma bai kamata a ce ma ya sansu ba.

Idan na tambaye shi ya aka yi ya san duk wadannan abubuwan, sai ya ce ai ni na gaya masa, kuma ya zarge ni da cewa na faye mantuwa," a cewar ta.

Amy - wadda ba sunanta na gaskiya ke nan ba ta fara mamakin yadda yake sanin duk inda ta je a kodayaushe.

"Wani lokacin sai ya ce mini ya ganni a wani wuri tare da kawayena, a lokacin da yake wucewa. Sai na fara shakka, na zama ba na amincewa da kowa hatta kawayena," in ji ta.

An kwashe watanni ana ci gaba da samun haka, har ya dinga shafar zamantakewar aurenmu wanda da ma can akwai cutarwa a cikinta. Tura ta kai bango ne a lokacin da muka yi wata tafiya gaba dayanmu.

"Mun kai ziyara wata gonar kabewa, a wani karshen mako da komai ya tafi lafiya-lafiya, wanda hakan ke nufin mijina bai takale ni ba. Danmu mai shekara shida yana wasa a kasa cike da farin ciki" a cewar Amy.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Mijina ya miko mini wayarsa don na ga wani hoton da ya dauka a wata gona, sai kawai na ga wani sako ya fado a saman wayarsa. Sakon na cewa 'Za ka iya ganin rahoto kan abubuwan da Amy Mac ke yi na yau da kullum.'"

"Kawai sai na ji na kalu, numfashina ya dauke na wani dan lokaci, sai na ce masa ina zuwa, na wayence kamar zani bandaki. Sai na nuna kamar ban ga komai ba saboda dana."

"Abu na farko da na yi shi ne sai na je dakin karatu na bude wata kwamfuta don duba sunan manhajar da yake amfani da ita. To a lokacin ne na fahimci komai, bayan shafe watanni ina tunanin ko dai na fara zautuwa ne. "

Stalkerware - wadda kuma aka fi sani da manhajar ma'aurata - manhaja ce mai matukar nagarta da ake amfani da ita wajen leken asiri kuma ana sayar da ita ne a shagunan intanet.

Tana nadar dukkan sakon kar ta kwana da duk wani abin da mutum yake yi a kan wayarsa, tana bibiyar inda mutum yake ta hanyar bin diddigin GPS da kuma kamarar waya don leken asirin abin da mutum ke yi.

Woman on phone
Getty
Sidestep stalkerware

Tips to avoid being victimised:

  • Don’t leavedevice unattended – most software requires physical access

  • Ditch fingerprintlock - a partner can use your print while you sleep

  • Add security app- antivirus software can also detect spyware and remove it

Source: BBC

A cewar wani kamfanin samar da tsaro a intanet na Kaspersky, yawan wadanda ke gane cewa an sanya musu manhajar a wayar salularsu na karuwa da kashi 35 cikin 100 a shekarar da ta wuce.

Masu bincike na Kaspersky sun ce fasahar kariyar da kamfanin ke da shi, ya sa sun gano manhajar, a kan na'urori 37,532 kawo yanzu a wannan shekarar.

Babban mai bincike, David Emm ya ce alkaluman ba su taka-kara sun karya ba".

"Mafiya yawan mutane suna kare kwamfutarsu ko kwamfutar tafi da gidanka, amma ba kasafai suke kare wayoyin salularsu ba," in ji shi.

"Mun samu wannan bayanai ne bayan mun sanya manhajarmu a kan wasu wayoyi, don haka wannan alkaluma ba su ma zo ko kusa da yawan abin da ake yi ba."

Kaspersky ya gano cewa kasar Rasha ita ce kasar da ta fi kowa samun masu amfani da manhajar Stalkerware.

Indiya da Brazil da Amurka da kuma Jamus suna cikin kasashe biyar da ke sahun gaba, sai kuma Burtaniya wadda take matsayin kasa ta takwas, inda kamfanin ya gano ana amfani da mahajar 730.

Wani kamfanin na daban da ke samar da tsaro a shafukan intanet ya ce, akwai hanyoyin da mutum zai iya bi idan ya gano cewa ana leken asirinsa.

"Yana da kyau a kodayaushe ka san irin manhajar da ke kan wayarka kuma ka dinga dubawa ko wayarka ta samu cutar Virus, idan akwai bukatar yin hakan. Sannan idan akwai wata manhajar da ke kan wayar ka da baka santa ba, yana da kyau ka bincika intanet don sanin ko wace iri ce kuma ka goge su," in ji Jake Moore, na kamfanin Eset.

"Abin na da ya fi dacewa shi ne duk manhajar da baka amfani da ita to ka goge ta."

Daga lokacin da Amy ta fahimci an yi mata leken asiri ta daina amincewa da duk wani abin da ya shafi fasaha, sai a yanzu ne abin ya fara yi mata dan sauki-sauki.

Kungiyoyin agaji sun ce mutum kan fara shiga irin wannan hali ne saboda kaduwar da suka yi.

Jessica ma an yi ta leken asirinta da manhajar ta Stalkerware. Tsohon mijinta ne ya dinga yi mata hakan, ta hanyar sauraron abin da take cewa a waya, ya dinga maimaita mata wasu kalmomin da ya ji ta fada a lokacin da take hira da kawayenta.

Ta kwashe shekaru da rabuwa da shi, amma har gobe idan ta fita da kawayenta sai ta kulle wayarta a mota.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana amfani da Stalkerware wajen sanin inda mutum ya ke da kuma karanta sakon karta kwana na wayarsa

Gemma Toynton, wadda ke aiki da kungiyar da ke yaki da cin zarafi a cikin gida ta Safer Places, ta ce ta sha ganin wadanda ke shiga wani matsanancin hali.

"Ta na janyo raguwar amincewa juna," in ji Gemma. " Ta kan sa su ga waya ko kwamfutar tafi da gidanka tamkar wani makami, saboda da su ake amfani.

"A zuciyarsu sun dauki fasaha tamkar wata ragaya da aka daure su da ita, haka kuma mutane da dama ne ke daina amfani da intanet.

"Lamarin na shafar baki daya rayuwa ne. kuma abin damuwa ne ganin amfani da wannan manhajar na karuwa. "

A yanzu Amy, wadda Ba'amurkiya ce aurenta ya mutu, kuma tana rayuwa a wani wuri mai nisa da inda tsohon mijinta yake.

Ta samu umarnin kotu da ta hana shi yin wata mu'amala ta kai tsaye da ita, kuma ta hanyar wasika ce kawai zai sanar da ita bayanai kan abin da ya shafi kula da dansu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu sanya manhajar na yin amfani da zanen yatsu su shiga wayar mutum su sanya masa manhajar a kan wayarsa

Kamfanonin da ke sayar da manhajar leken asirin dai suna yi ne don sa ido a kan ma'aikata ko kuma don iyaye su sa ido a kan yaransu.

A kasashe da dama ciki har da Burtaniya yin amfani da manhajar wajen leken asirin matarka ya sabawa doka. Don haka mafiya yawan kamfanonin su kan bayyana karara cewa babu ruwansu da duk wanda ya yi haka.

Kodayake wasu daga cikin kamfanonin an yi amfani da shafinsu a wasu makaloli da wasu farfesoshi suka rubuta, inda suka bayar da shawarar yin amfani da manhajar wajen leken asisrin matan da ke cin amanar mazajensu na aure.