Daga Saudiyya Buhari zai wuce Landan

A

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

A watan Afrilu ma Shugaba Buhari ya je Landan a wata tafiya ta kashin kai inda ya shafe kwana 10

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai wuce birnin Landan a ranar Asabar bayan ya kammala abin da ya kai shi Saudiyya.

Mai taimaka wa shugaban kasar kan yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce shugaban kasar zai shafe mako biyu a Landan a wata tafiya ta kashin kai da zai yi.

Mista Adesina ya ce "Shugaba Buhari zai bar Najeriya a yau Litinin kan wata tafiyar aiki zuwa Saudiyya don halartar taron zuba jari karo na uku da kasar ke jagoranta a birnin Riyadh.

"Shugaba Buhari zai gana da Sarki Salman da Sarki Abdullah na Jordan a yayin tafiyar.

"Sannan a ranar Laraba zai halarci wani taron duk a Riyadh mai take "Afirka ina muka dosa: Yaya zuba jari da kawo sauyi a fannin kasuwanci a nahiyar? Tare da shugabannin Kenya da Congo-Brazzaville da kuma Burkina Faso," in ji sanarwar.

Bayan ya kammala ne zai wuce Birtaniya sannan ana sa ran zai koma Najeriya ranar 17 ga watan Nuwambar 2019.

A watan Afrilu ma Shugaba Buhari ya je Landan a wata tafiya ta kashin kai inda ya shafe kwana 10.

A shekarar 2017 ne Buhari ya shafe wata uku a Landan yana jinya, al'amarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar.