Har yanzu ba a ceto dan shekara biyu daga rijiya ba

Sujith on his mother's arm with his brother and father
Bayanan hoto,

Sujith dan shekaru biyu ne inda fadawarsa rijiya ke ci gaba da girigiza duniya

Masu aikin ceto sun shiga kwana na hudu a ci gaba da fafautukar ganin an ceto wani yaro dan shekaru biyu da ya fada a rijiya a India.

Da farko dai Sujith Wilson, ya kasance a nisan gaba 30 a rijiyar to amma daga baya ya sake lulukawa cikin rijiyar mai zurfin mita 180 da ke Tamil Nadu.

Masu aikin ceton na ta faman antaya iskar Oxygen ga yaron wanda ke cikin rijiyar duk da cewa ba sa iya sanin hakikanin halin da yake ciki saboda lakar da ke tsakaninsu da yaron.

Yanzu haka masu aikin ceto na amfani da manyan injinan haka rami domin samar da wani ramin a kusa da rijiyar da yaron ya fada.

A ranar Juma'a Sujith dai ya fada a tsohuwar rijiyar ne a lokacin da yake wasa tare da abokansa.

'Yan jarida sun ce mahaifiyar yaron ta je bakin rijiyar inda ta yi ta kiran sunan yaron nata tana lallashinsa da ya yi shiru.

Tun da farko dai an ga mahaifiyar Sujith tana dinka jakar da take fatan ta yi amfani da ita wajen fito da yaron daga rijiyar.

Al'amarin yaron dai ya ja hankalin al'ummar India, inda a ranar Litinin din nan firai ministan kasar, Narendra Modi ya wallafa alhininsa dangane da halin da yaron yake ciki, a shafinsa na Twitter: