Buhari na raina wa 'yan Najeriya wayo - PDP

A

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

A watan Afrilu ma Shugaba Buhari ya je Landan a wata tafiya ta kashin kai inda ya shafe kwana 10

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce yawan fita kasashen waje da Shugaba Muhammadu Buhari yake yi 'bata kudaden Najeriya ne'.

Shugaba Muhammadu Buhari dai na kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya domin halartar wani taro na bunkasa tattalin arzikin kasashen duniya.

Kasar Saudiyya ce ta dauki nauyin shirya taron, kuma ana sa ran shugaban zai gabatar da jawabi a matsayinsa na jagora daga nahiyar Afirka.

Sai dai shugaba Muhammadu Buharin ya daka-gari zuwa kasar Saudiyyar ne, kwana biyu da dawowarsa daga kasar Rasha, lamarin da ya fara jan hankalin abokan hamayyar gwamnatinsa.

Sai dai jam'iyyar adawa ta PDP ta bakin mai magana da yawun jam'iyyar, Senata Umaru Tsauri ta ce babu wata riba ga kasar.

Latsa wannan alamar lasifikar domin sauraron bayanin Sanata Umar Tsauri.

Bayanan sauti

Sanata Umar Tsauri

To sai dai mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu ya ce taron da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai halarta a kasar Saudiyyar taro ne mai muhimmanci saboda irin batutuwan da za a tattauna:

Tafiye-tafiyen da shugaban Muhammadu Buhari ke yi dai sun dade suna janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya tun hawansa kan karagar mulki.

Wani sharhi da wata jaridar kasar ta yi ya nuna cewa shugaban kasar ya cinye kusan kashi daya bisa ukun shekara uku da ya yi na farkon wa`adin mulkinsa ne yana bulaguron jinya.

Ko da a watanni ukun da suka wuce, shugaban kasar ya fice daga Najeriyar har sau hudu, inda ya ziyarci kasashen Japan,da Rasha, da Afirka ta kudu da kuma Amurka.