Fursunoni 153 sun tsere daga gidan yari a jihar Kogi

Prisoners

Rundunar 'yan sandan jihar Kogi a Najeriya, ta ce tuni ta samu zarafin cafke fursunoni 31 daga cikin 153 da suka tsere daga gidan yarin garin Koton Karfe na jihar Kogi.

Da misalin karfe 5:00 na safiyar ranar Litinin ne dai fursunonin suka tsinke bayan da ruwa kamar da bakin kwarya ya rusa wani bangare na ginin gidan yarin.

To sai dai kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Williams Obe Aya, ya shaida wa BBC cewa bayan tserewar fursunonin ne hukumar ta nemi daukin wasu hukumomi da 'yan banga domin shawo kan fusrsunonin.

DSP Williams ya kara da cewa kawo yanzu jami'an nasu bisa hadin gwiwar 'yan sintiri sun samu nasarar cafke mutum 31, kuma tuni aka mayar da su gidan yarin.

Sai dai ya ce jami'an nasu na ci gaba da farautar ragowar fursunoni 122 wadanda suka bazama daji.