Masana kimiya sun ce Botswana ne 'asalin mutanen wannan lokaci'

Tafkin da ya bushe ya koma gishiri

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tafkin da ya bushe ya koma gishiri

Masana kimiyya sun ce tushe ko kuma asalin mutanen wannan lokaci a duniya shi ne wani yanki da ke kudu da kogin Zambesi a kasar Botswana.

Masanan sun ce gishiri ne yanzu ya mamaye yankin amma kuma wani lokaci can baya, tafki ne da ke iya zama tushen mutanen wannan lokaci shekaru dubu dari biyu da suka wuce.

Masu bincken sun ce mutane sun zauna a wurin shekaru 70,000 kafin samun canjin yanayi.

A wancan lokacin, mutanen da ke zaune a yankin sun fara matsawa daga wajen abin da ya bayar da kafar ficewa daga Nahiyar Afrika, a cewar masanan.

"An dade da gano al'ummar wannan lokacin nahiyar Afirka ne tushensu shekaru dubu dari biyu baya," a cewar farfesa Venessa Hayes na cibiyar gudanar da bincike a Australia.

Ta kara da cewa abin da aka dade ana tafka mahawara akai shi ne ainihin wajen da aka gano hakan da kuma yadda mutanen baya suka warwatsu.

A cewar ta, wannan bincike ya sanya sauran masu bincike yin tantama kan nazarin da aka gudanar.

Masu binciken na ganin mutanen da suka gabaci al'ummar yanzu sun samu mazauni kusa da wani makeken tafkin nahiyar Afirka da aka fi sani da tafkin Makgadikgadi, wanda a yanzu gishiri ke mamaye da shi.

"Babban waje ne mai fadin gaske, da ya kasance mai danshi. Wajen zai yi dadin zama ga mutanen yanzu da namun daji," in ji Farfesa Hayes.

Masanan sun ce bayan zama a wajen na kusan shekaru dubu saba'in, mutane suka fara yin kaura.

Kuma sauyin yanayi a lokacin damina ya sanya mutane ficewa daga yankin shekaru dubu dari da talatin da kuma dubu dari da goma da suka gabata.

Asalin hoton, CHRIS BENNETT, EVOLVING PICTURE, SYDNEY, AUSTRALIA

Bayanan hoto,

Farfesa Hayes tana koyon yadda ake hada wuta da maharban Jul'hoansi a dajin Kalahari da ke Namibia

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mutanen farko da suka yi hijira sun tsinci kansu a yankin arewa maso gabas sai gwamman mutanen da suka sake ficewa daga yankin da suka yi tafiya zuwa kudu maso yamma sannan kashi na uku na 'yan gudun hijirar suka ci gaba da zama a yankin har zuwa wannan lokaci.

Wannan abu dai ya karkata ne ga gano tushen mutanen da suka zauna a wajen ta hanyar yin amfani da kwayoyin halittan 'yan Afirkan da ke raye.

Tattara abubuwan da suka shafi batun gado na jini da kuma yanayi, masu bincike sun iya samun hotunan yadda nahiyar Afirka ta ke shekaru dubu dari biyu da suka gabata.

Sauya labarin asalin mutane

Sai dai kuma, wani kwararre ya yi gargadi bayan da aka wallafa binciken a mujallar Nature, inda yake cewa ''wa ya ce ba za a iya sauya labarin asalin mutane daga kwayoyin halitta kadai ba?

Sauran nazarce-nazarcen da aka yi sun kara bada amsoshi daban-daban inda aka gano wasu abubuwa na mutanen da ke nuna cewa asalin mutanen baya shi ne gabashin Afirka.

Farfesa Chris Stringer na gidan adana kayan tarihi a birnin London wanda ba shi da alaka da binciken, ya ce asalin mutane wani abu ne mai wahalar ganewa.

''Ba zama ka iya yin amfani da kwayoyin halitta na DNA ba wajen gano wani waje daya da za a ce nan ne asalin mutane'' kamar yadda ya shaida wa BBC.

Farfesan ya kara da cewa ta yiyu akwai wasu wuraren da masu binciken ba su nazarta ba yayin gudanar da bincikennasu, wanda a cewarshi yin amfani da dalili daya ba zai zama shi ne gaskiyar bincike ba.