Dan shekara 84 ya kai hari Masallaci a Faransa

'Yan sandan Faransa da jama'a sun tsattsaya a wajen masallacin na Bayonne bayan mutane biyu sun jikkata sakamakon harbe-harbe.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dan bindigar na kokarin cinna wa kofofin masallacin wuta lokacin da wasu mutum biyu suka yi masa ba zato.

'Yan sandan Faransa sun ce sun kama wani dattijo mai shekara 84 da ake zarginsa da buda wuta a harabar wani masallaci a Faransa.

Ana zargin dan bindigar da kokarin cinnawa masallacin wuta tare da harbin wasu mutum biyu da shekarunsu ya kai 70 bayan da suka yi masa ba zata, kamar yadda 'yan sanda suka tabbatar.

Mutanen biyu sun jikkata sakamakon al'amarin da ya faru da karfe biyu da minti ashirin agogon GMT kuma tuni aka garzaya da su asibiti.

Bayan al'amarin ne kuma 'yan sanda suka cafke Maharin mai shekara 84 a kusa da gidansa da ke Bayonne.

Cikin wata sanarwa da 'yan sandan suka fitar sun ce maharin ya kuma yi kokarin kona wata mota a lokacin da ya fice daga harabar masallacin.

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya yi Allah wadai da harin wanda ya bayyana a matsayin abin takaici.

"Faransa ba ta maraba da masu nuna kyama," in ji shi

Shugaban ya ce za a hukunta wadanda ke da hannu a harin tare da kare musulman kasar.