'Yadda ruwa ya tafi da budurwata a Kaduna kafin aurenmu'

Bayanan sauti

Hira da saurayin da ruwa ya tafi da budurwarsa a Kaduna

Latsa lasifikar da ke sama don sauraron halin da saurayin ke ciki a hirarsa da Buhari Muhammd Fagge na BBC.

Al'ummar yankin Rigasa cikin jihar Kaduna sun fada cikin jimami da zulumi tun bayan batan mutum hudu ciki har da wata budurwa wadda kwanaki kalilan ya rage a daura mata aure.

Iftila'in ya faru ne ranar Litinin bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi awon gaba da abin hawan da suke tafiya a cikinsa da yammacin Lahadin da ta gabata.

Farida Saminu Abdullahi tana kan hanyarta ta zuwa unguwa ne, lokacin da al'amarin ya auku, kuma har zuwa daren Litinin, ba a iya gano ta ba.

Saurayin yarinyar, Mubarak Ibrahim Abubakar ya shaida wa BBC cewa tun ranar Litinin din ake nema amma Allah bai sa an dace ba, "don har kauyukan da ke makwabtaka da mu an kai cigiya amma shiru ba labari.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Duk da cewa watan 10 wato Oktoba ya kusa karewa har yanzu ana zabga ruwan sama a wasu sassa na arewacin Najeriya

"Har sarakan ruwa da na su duk an gaya musu lamarin. Kuma daga bangaren iyayenta har namu duk abin da ake kenan aikin nema," in ji Mubarak.

Saurayin ya fadi irin halin tashin hankalin da yake ciki "wallahi ina cikin tashin hankali, na kasa ci na kasa sha. Ko rufe idona na yi zan yi bacci sai Farida ta fado min na dinga tambayar kaina wane hali take ciki.

"Dazu da safe an samu rahoton samo mutum daya wanda shi ba mu tabbatar ko yana daya daga cikin wadanda suka bata tare da Farida ko kuma shi ma daga wani wajen ruwan ya taho da shi ba.

"Farida ta mutu ko tana da rai ko 'yan ruwa sun dauke ta? Fatana na san halin da take ciki, idan ta mutu to Alhamdulillah mun san ta yi shahada. Idan kuma tana da rai to Allah ya bayyana mana ita," a cewar Mubarak.

Duk da cewa watan 10 wato Oktoba ya kusa karewa har yanzu ana zabga ruwan sama a wasu sassa na arewacin Najeriya, al'amarin da ba kasafai yake faruwa ba.