Saudiyya ta jinjina wa Amurka kan kisan Al-Baghdadi

al-Baghdadi

Asalin hoton, AFP

Saudiyya ta jinjina wa Amurka kan abin da ya jawo kashe shugaban kungiyar IS Abu Bakr Al-Baghdadi a ranar Lahadi.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Hukumar Yada Labaran kasar SPA ta fitar, wacce jaridar Saudi Gazette ta ruwaito tana ambatar wata majiyar Ma'aikatar Harkokin Wajen Kasar inda ta ce gwamnatin Saudiyyar ta yi hakan ne bayan da Amurka ta sanar da kawar da Al-Baghdadi.

Sanarwar ta ce "Gwamnatin Saudiyya ta yaba wa namijin kokarin Amurka na fatattakar mambobin kungiyar 'yan ta'adda mai matukar hadari, wacce ta yi ta kokarin bata ainihin akidar Musulunci da Musulmai a fadin duniya, ta kuma yi ta aiwatar da mugayen ayyuka da suka saba wa darajar dan adam a kasashe da dama da suka hada da Saudiyyar."

Majiyar ta jaddada cewa Masauratar Saudiyya na ci gaba da kokari tare da kawayenta da Amurka ke jagoranta na daile ta'addanci, da toshe duk wata kafar yin sa da kuma yin fito na fito da masu akidar.

Bayanan hoto,

Masu fada a jin gwamnatin Amurka

A ranar Lahadi ne Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da cewa Al-Baghdadi "ya yi mutuwa irin ta karnuka" a wani hari da wasu dakarun Amurka na musamman suka kai a Syria.

Mutuwar jagoran kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi ta zama nasara ga shugaban Amurka Donald Trump, a yayin da yake fuskantar kakkausar suka kan matakinsa na janye dakarun Amurka daga arewa maso yammacin Syria - da kuma kokarin kalubalantar binciken tsige shi da jam'iyyar Democrats ke yi.

Amma kawayen Amurka sun ce kisan al-Baghdadi ba yana nufin yaki da kungiyar ta IS ya zo karshe ba ne.

Al-Baghdadi ya kashe kansa da yaransa uku bayan ya tayar da bam din da ke jikinsa in ji Mista Trump wanda ya ja hanyar karkashin kasar da ya bi ta fashe.

Babu wani sojan Amurka da ya rasa ransa sakamakon tashin bam din sai dai daya daga cikin karnukan sojojin Amurkar ya raunata matuka.

Shugaban kasar ya bayyana cewa fashewar bam din ya tarwatsa sassan jikin al-Baghdadi, kuma wani gwajin kwayoyin halitta da aka gudanar da wurin da lamarin ya faru ya tabbatar da cewa lallai shi ne ya mutu.

Ya duniya ta dauki mutuwar al-Baghdadi?

Shugabanni a fadin duniya sun mayar da martani dangane da mutuwar Abu Bakr al-Baghdadi inda da dama daga cikinsu ke cewa za a ci gaba da yaki da kungiyar IS.

Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana mutuwar al-Baghdadii a matsayin ''wani muhimmin abu a fadan da ake yi da ta'addanci amma fadan da ake yi da IS bai kare ba.''

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana wannan ci gaba a matsayin wata ''babbar nasara'' da aka samu kan IS amma ''za a ci gaba da yakarsu har sai an tarwatsa kungiyar 'yan ta'addan.''

Sojoji na musamman da suka kai sumamen sun shafe kusan sa'o'i biyu a wurin suna tattara bayanai kuma sun samu bayanai da abubuwa matuka inji shugaban.

A ranar Lahadi, mayakan Kurdawa na SDF sun bayyana cewa mai magana da yawun Kungiyar IS Abu al-Hassan al-Muhajir wanda na hannun daman al-Baghdadi ne an kashe shi a wani harin hadin gwiwa da Amurkar ta kai kusa da garin Jarablus na Syria.

Karin Labaran da za ku so ku karanta