Dan shekara 12 ya fara karatun jami'a a Ghana

  • Daga Favour Nunoo
  • BBC News Pidgin, Ghana
Viemens Bamfo

Asalin hoton, Facebook

Viemans Bamfo mai shekara 12 dan kasar Ghana ya janyo ka-ce-na-ce a shafukan sada zumunta bayan da ta bayyana cewa ya samu gurbin shiga jami'a.

Yanzu haka dai Bamfo ne mafi karancin shekaru a cikin dalibai 2900 da suka samu gurbin shiga jami'a a kasar a bana.

Viemens Bamfo dai bai ci gaba da sakandare ba bayan kare firamare, inda mahaifansa ke kowaya masa karatu a gida.

Daga nan ne kuma ya rubuta jarrabawar samun shaidar kammala karatun sakandare, inda ya samu kyakkyawan sakamakon WASSCE.

Tuni Viemans ya fara karatu a sashen sanin makamar aikin gwamnati wato Public Administration a jami'ar University of Ghana.

Hakan ne dai ya sa masu amfani da kafafen sada zumunta suka yi ta sukar al'amarin, inda suke bayyana mamakinsu kan yadda yaron da bai yi sakandare ba zai lashe jarabawar sakandare kuma har ya shiga jami'a.