An sato tufafinsa Al-Baghdadi don tabbatar da DNA dinsa

Al-baghdadi na yin jawabi a gaban wani taro a Mosul, a 2014

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Al-baghdadi ya sanar da kafa "daula" daga Mosul a 2014

Mayakan Kurdawa na SDF a Syria sun ce jami'ansu na leken asiri sun sace kananan kayan Abu Bakr al-Baghdadi, wanda daga bisani aka yi amfani da su wurin yin gwaje-gwajen da suka tabbatar da kwayar halittarsa ta DNA kafin a kashe shi.

Wani babban kwamandan SDF Polat Can ya ce 'yan leken asirin sun taka muhimmiyar rawa wajen lura da kai-komon shugaban IS din gabanin harin da dakarun Amurka suka kai a Syria.

Baghdadi ya kashe kansa a harin.

Shugaban Amurka Donald Trump bai ba da muhimmanci ga rawar da mayakan Kurdawa suka taka ba.

Da yake sanar da harin da aka kai a ranar 27 ga watan Oktoba, Mista Trump ya ce Kurdawan sun "taimaka" da bayanai, amma ya kara da cewa Kurdawan basu dauki matakin soji ba.

Amma a wani jerin sakonni da ya wallafa a Tuwita a ranar Litinin, Mista Can ya dage cewa mayakan SDF sun ba da gagarumar gudunmuwa a harin.

"Dukkan bayanan sirri, da iya kaiwa ga Al-baghdadi da yadda aka gano wurin da yake, sun samu ne sakamakon aikin da muka yi. Jami'anmu na tara bayanan sirrin sun taimaka wurin tura bayanan inda yake, da yadda aka kai harin saman. Hakan ya taimaka aka samu nasara daga farko har karshe," a cewarsa.

Mista Can ya kara da cewa SDF ta dade tana aiki tare da CIA wurin bibiyar zirga-zirgar al-Baghdadi tun 15 ga watan Mayu, kuma ta gano maboyarsa a yankin Idlib, inda aka kai masa harin.

Ya ce majiyar SDF ta gano cewa shugaban IS din na dab da komawa Jarablus da zama.

SDF na daga cikin manyan kawayen Amurka a yakin da suke yi da kuniygar IS, amma daga baya a cikin watan Oktoba, Mista Trump ya janye dakarun Amurka daga arewacin Syria.

Masu sharhi na ganin janye dakarun da Amurka ta yi ya bai wa Turkiyya damar fara kai hare-hare a kan mayakan Kurdawa a Syria.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Me za mu yi game da kai harin?

An sanar da kawayen Amurka da dama a yankin game kai harin, cikinsu har da Turkiyya da Iraqi da mayakan Kurdawa a Arewa maso-gabashin Syria da Rasha wadda ke gudanar da sararin samaniya a Idlib.

Rahotanni na cewa mayakan Amurka sun yi ta ruwan albarusai ta kasa.

Suna sauka wurin, sai suka bukaci al-Baghdadi wanda ya tsere ya boye a cikin bututun karkashin kasa ya fito ya mika wuya.

Sojojin sun huda ramukan bangon wurin domin kawar da tarkon da za a iya yi musu a jikin kofa.

Da ganin haka, sai al-Baghdadi ya tayar da jigidar kunar bakin waken da ke sanye a jikinsa, wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa da yara uku.

Turmp ya ce gwaje-gwajen da aka yi kan gawar sun tabbatar da cewa al-Baghdadi ne.

Kwararrun da ke dauke da samfurin kwayar hallitar DNA ta al-Baghdadi da suka raka sojojin Amurkan ne suka gudanar da gwajin, a cewar rahotanni, kuma wadanda suka dawo da yawancin bangaren jikin gawar a jirgi mai saukar ungulu mai dauke da na'urar gane fuska da kuma tantance kwayar halittar dan Adam.

A ranar Litinin, babban kwamandan rundunar tsaron Amurka, Janar Mike Milley ya ce jami'an Amurka sun bizne gawar al-Baghdadi.

Ya ce yanzu an kammala bizne gawar al-Baghdadi yadda ya dace, ba tare da ba da karin bayani ba.

Wani jami'i ya sheda wa kamfanin dillancin labaru na Reuters cewa an yi jana'izar al-Baghdadi daidai da yadda Musulunci ya tanada, sannan aka bizne shi a teku.

Irin haka aka yi wa tsohon Shugaban kungiyar Al-qaeda, Osama bin Laden a Pakistan a 2011.