Jerin tafiye-tafiyen Buhari cikin shekara biyar

Buhari

Idan akwai wani batu da aka tayar da kura a makon nan, shi ne na tashin Shugaba Muhammadu Buhari zuwa kasar Saudiyya domin halartar wani taron kasuwanci, inda daga nan zai wuce zuwa birnin Landan, kafin daga bisani ya koma Najeriya a ranar 17 ga Nuwamba.

A ranar Asabar din nan ne ake sa ran Shugaba Buharin zai bar kasar Saudiyya zuwa Birtaniya domin kai wata ziyarar radin-kai inda zai kwashe kwana 17.

Idan har Buhari ya koma Najeriya a ranar 17 ga watan Nuwamba, to lissafi zai kama kwanaki 425 ke nan shugaban ya yi a kasashen waje a tsawon shekara hudu da rabi na mulkinsa.

BBC Hausa ta duba kundinta tare da samun karin wasu bayanai daga jaridar Daily Trust dangane da kwanakin da shugaban ya yi a wajen Najeriya, kamar haka:

2015

 • 3 Yuni - Niamey - Niger - Taron koli kan Boko Haram (tafiyar Buhari kasar waje mako guda bayan shan rantsuwa)
 • 4 Yuni - N'Djamena - Chad - Ziyarar aiki
 • 7 - 8 Yuni - Munich - Germany - Taron koli na kasashen G7 na 42
 • 12 - 13 Yuni - Johannesburg - Afirka ta Kudu - Taron Tarayyar Afirka na 25
 • 19 - 23 Yuli - Washington, D.C. - Amurka - Ziyarar aiki
 • 29 - 30 Yuli - Yaoundé - Cameroon - Ziyarar aiki
 • 2 - 3 Agusta - Cotonou - Benin - Bikin 'yancin kai
 • 7 Satumba - Accra - Ghana - Ziyarar aiki
 • 14 - 16 Satumba - Paris- Faransa - Ziyarar aiki
 • 24 - 29 Satumba - New York City - Amurka - Babban taron Majalisar DInkin Duniya na 70
 • 26 - 30 Oktoba - New Delhi - India - Taron koli na India da Afirka na uku
 • 30 Oktoba - Khartoum - Sudan - Ziyarar aiki
 • 22 - 24 Nuwamba - Tehran - Iran - Taron kasashe masu fitar da iskar Gas na uku
 • 28 - 30 Nuwamba - Valletta - Malta - Taron kasashe rainon Ingila na 2015
 • 30 Nuwamba - 1 Disamba - Paris - Faransa - Taron kungiyoyin Paris na 21
 • 4 - 5 Disamba - Johannesburg - South Africa - Taron koli na China da Afirka
 • 10 December -Benin Republic - Jana'izar Shugaba Mathieu Kerekou

2016

 • 8 Janairu - Benin- Cotonou - Taron koli na Shugabannin kasashen da ke kewaye da ruwan Nijar kaso na 11
 • 17 - 20 Janairi - Abu Dhabi - Dubai - Taron koli kan makamashi
 • 26 Janairu - Addis Ababa - Ethiopia - Taron shugabannin kasashen Tarayyar Afirka na 26.
 • 27 - 29 Janairu - Eldoret, Nairobi - Kenya - Ziyarar aiki.
 • 2 - 4 Fabrairu - Strasbourg - Faransa - Ziyarar aiki
 • 5 - 10 Fabrairu - London - Birtaniya - Hutu
 • 18 Fabrairu - Sharm El Sheikh - Egypt - Taron Afirka na 2016'
 • 22 - 27 Fabrairu - Riyadh, Jiddah, Makka, Madina - Saudiyya - Ziyarar aiki
 • 27 - 28 Fabrairu - Doha- Qatar- Taron Kungiyar OPEC
 • 14 Maris - Malabo - Equatorial Guinea - Ziyarar aiki
 • 30 Maris - 3 Afrilu - Washington, D.C. - Amurka - Taron koli kan nukiliya na 4
 • 11 - 14 Afrilu - Beijing - China - Ziyarar aiki
 • 13 Mayu - 15 Mayu - London - Birtaniya - Taron koli kan rashawa da cin hanci
 • 6 - 19 Yuni - London - Birtaniya - Jinyar rashin lafiya
 • 8 Agusta - N'Djamena - Chad - Rantsar da Shugaba Idris Deby
 • 27 - 28 Agusta - Nairobi - Kenya - Taron Tokyo kan Afirka
 • 13 - 16 Oktoba - Berlin - Jamus - Ziyarar aiki
 • 14 - 18 Nuwamba - Marrakesh - Morocco - Taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi
 • 22 Nuwamba - Equitorial Guinea - Taron kasashen Afirka da na Larabawa karo na hudu
 • 5 - 7 Disamba - Dakar - Senegal - Taron kasashen duniya kan zaman lafiya da tsaro a Afirka
 • 13 Disamba - Banjul - Gambia - Taron koli na ECOWAS

2017

 • 7 Janairu - Accra - Ghana - Rantsar da Shugaba Nana Akufo-Addo
 • 12 Janairu - Banjul - Gambia - Taron sulhu na ECOWAS
 • 13 - 14 Janairu - Bamako - Mali - Taron koli tsakanin Afirka da Faransa
 • 19 Janairu - 30 Maris - Landan - Birtaniya - Hutu da jinya
 • 7 Mayu - 13 August - Landon - Jinya
 • 17-21 Satumba - Amurka - Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72
 • 21- 25 Satumba - London - Birtaniya - Hutu
 • 18 - 22 Oktoba - Santambul - Turkiyya - Ziyarar aiki da taron kasashe takwas masu tasowa
 • 24 Oktoba -Yamai - Jamhuriyar Nijar - Taro kan samar da kudin bai daya na kungiyar ECOWAS
 • 28 Nuwamba - Abidjan, Cote d'voire - taron Tarayyar Afirka da Tarayyar Turai karo na biyar.
 • 11 Disamba - Paris - Faransa - Taron koli kan sauyin yanayi
 • 18 Disamba - Yamai - Niger - Bikin 'yancin kai na 59

2018

 • 26- 30 Janairu Addis Ababa - Ethiopia - Taron shugabannin kasashen Tarayyar Afirka na 30
 • 5 Maris -Ghana - Bikin samun 'yancin kai
 • 9 Afrilu 19 - Landan - Birtaniya - Taron shugabannin kasashen renon Ingila
 • 28 - 30 Afrilu - Washington - Amurka - Ziyarar aiki.
 • 1 - 2 Mayu - Landan - Birtaniya - Yada zango
 • 8 - 12 Mayu - Landan - Birtaniya - Ganin likita
 • 10 - 12 Yuni -Morocco - Ziyarar aiki
 • 30 Yuli-2 Yuni -Mauritania - Taron shugabannin kasashen Tarayyar Turai
 • 15 - 18Netherlands - taron amincewa da dokokin kotun ICC a Hague
 • 29 - 31 Yuli - Lome - Togo - Halartar taron ECOWAS.
 • 3 - 13 - London - Birtaniya - Hutu
 • 31 Agusta - 3 Satumba - China - Taron Afirka da China karo na 7
 • 23 - 29 Satumba -Amurka - Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 73
 • 9 Nuwamba - Faransa - Taron farko na Paris
 • 23 Nuwamba - N'Djamena - Chad - Taro kan Boko Haram
 • 2-3 Disamba - Kraków - Poland - Ziyarar aiki.

2019

 • 1 Afrilu - Dakar - Rantsar da Shugaba Macky Sall1
 • 4-6 Afrilu - Jordan - Taron tattalin arziki na duniya kan Afirka ta arewa da gabas ta tsakiya
 • 7-11 Afrilu - Dubai - Taron zuba jari karo na 9
 • 13 Afrilu - Nd'jamena - Taron shugabannin kasashen Sahel
 • 25 -5 Mayu - Landan - Birtaniya - Hutu
 • 16 - 5 Mayu -Saudiyya - Aikin Umara
 • 30- 2 Yuni - Saudiyya - Taron kungiyar kasashen musulmai
 • 6-2 Yamai - Taron Tarayyar Turai kan kasuwancin bai daya
 • 26 Yuli -Liberia - Bikin samun 'yancin kai
 • 25-30 -Japan - Taro kan alakar Tokyo da Afirka
 • 14 Satumba - Burkina Faso - Taron ECOWAS kan ta'addanci
 • 25 Satumba - 1 Oktoba - New York City - US - Ziyarar aiki.
 • 2-3 Oktoba - Pretoria - Afirka ta Kudu - Ziyarar aiki
 • 21-23 Oktoba - Sochi - Rasha
 • 28 - 31 Oktoba - Riyadh - Saudiyya - Taron kasuwanci
 • 31 - 17 Nuwamba - London - Burtaniya - Ziyara don kai

Za a iya cewa idan aka hada kwanakin wuri guda to Shugaba Buhari ya kwashe fiye da shekara guda ba ya cikin kasar.

Hakan ne ya sa 'yan kasar fadin albarkacin bakinsu, inda aka samu bangarori biyu na masu suka da yabon irin tafiye-tafiyen da shugaban yake yi.

Tuni dai jam'iyyar PDP, ta bakin mai magana da yawunta, Sanata Ibrahim Tsauri, ta ce tafiye-tafiyen tamkar "raina wa 'yan Najeriya hankali" ne.

To sai dai fadar shugaban ta ce tafiye-tafiyen na da alfanu sosai ga tattalin arzikin kasar.

Har wa yau, masana kimiyyar siyasa irin su Dakta Abubakar Kari na jami'ar Abuja ya ce "tafiye-tafiyen na da alfanu a diflomasiyyance da kuma tattalin arzikin kasar."

Sai dai ya kara da cewa " har yanzu 'yan Najeriya ba su gani a kasa ba kasancewar babu wani alfanu da tafiye-tafiyen suka janyo wa kasar."

Labarai masu alaka