Zabtarewar kasa: Mutum 40 sun mutu ana neman 13 a Kamaru

South Africa

Akalla mutum 42 ne suka mutu sakamakon zabtarewar kasa da aka samu a daren ranar Litinin a garin Baffoussam da ke yammacin birnin Younde.

Har wa yau, masu aikin ceto na can na neman mutum 13 da har yanzu ba a gan su ba tun bayan zaftarewar kasar, inda mutum shida suka jikkata.

Ibtila'in ya kuma shafe gidaje 11 daga cikin kusan 30 da al'amarin ya shafa, inda mutum 130 suka rasa matsugunansu.

Yanzu dai an killace wannan wurin, kuma ana sa ran tsaiyar da matakan da za a dauka nan gaba a yammacin ranar Laraba.

Gwamnan lardin, Mr Augustine ya ce mutanen da abin ya shafa sun yi gine-gine a kan tsaunuka duk da irin gargadin da gwamnati ta yi cewa a guji tsaunuka kasancewar za a samu ruwa kamar da bakin kwarya.

Har kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga hukumar agaji kan faruwar al'amarin, sai dai gwamnan lardin ya nuna cewa za a yi bincike.