Kwastam sun kama shinkafar biliyan 286 a bana

Rice
Bayanan hoto,

Rubabbiyar shinkafar da aka shigo da ita Najeriya daga China da Ghana

Hukumar yaki da fasa kwauri a Nijeriya ta fitar da adadin yawan kudin rubabbiyar shinkafa da aka shigo da ita Naijeriya daga Ghana da kuma kasar Sin wato China.

A wata sanarwa da aka mekawa BBC, shugaban hukumar kanar Hamid Ali mai ritaya yace an kama kwantaina hamsin da hudu makarare da rubabbiyar shinkafa da kwayar Tramadol.

Daga Janairun bana kawo yanzu hukumar ta kwace yawan shinkafa da adadin kudinta ya haura naira biliyan 286.

Naijeriya dai ta haramta shigo da shinkafa ta kan tudu, a yunkurin gwamnatin kasar na bunkasa nomanta a cikin gida.

Yau dai kamar watanni uku ke nan gwamnatin kasar ta rufe iyakokinta da kasashen da take makwabta da su wanda babu shiga ko fita da kayayyaki sai dai ta kan ruwa.

Wannan mataki kamar wasu ke kallo ya fara shafar tattalin arzikin wasu daga kasashe da ke makwabtaka da Najeriya.

Ko a ranar talatar hukumar kwastam ta ce ta kama kontaina 53 makare da kwayoyin tramadol da gurbatacciyar shinkafa da kudinsu ya wuce naira bilyan biyu da aka shigar kasar daga Ghana da China.

Shugaban hukumar yaki da fasa kwauri ta Najeriya, Col Hamid Ali ya ce shinkafar dai wadda aka kama ta a birnin Legas ta lalace amma duk da haka wasu 'yan kasuwa sun sauya wa shinkafar buhu domin nuna cewa shinkafar ta Najeriya ce.

Wannan dai shi ne wani kame mafi girma mai yawan kwantainoni 53 da aka kama bayan rufe iyakokin Najeriya.

Kame na farko dai ya zo da hukumar fasa kwauri mai kula da iyakokin Oyo da Osun tayi ta tabar wiwi ta kimanin miliyan dari.

Gwamnatin tarayya dai ta karyata rahotannin da ke cewa rufe bakin iyakar ya tona asirin Najeriya cewa yawan shinkafar da take nomawa ba ta isa ta ciyar da 'yan kasar ba har a sayar ga kasashen da ake makwabtaka da su ba.

Daga karshe Col Hamid Ali ya kara da cewa sun samu rahotannin da ke cewar kasar Benin ta yi odar shinkafa daga Japan ta kimanin dala miliyan $32,000,000, domin shigar da ita Najeriya.