Kotun koli ta kori karar Atiku kan Buhari

Buhari Atiku

Kotun koli ta Najeriya ta kori karar da jam'iyyar PDP da dan takarar shugabancin kasar jam'iyyar, Alhaji Atiku Abubakar suka shigar gabanta suna kalubalantar nasarar da hukumar INEC ta bai wa shugaba Buhari a zaben 2019.

Alkalan kotun dai sun yi watsi da karar ne bisa rashin dacewarta a ranar Laraba.

A ranar 11 ga watan da ya gabata ne dai kotun sauraron kararrakin zabe ta yi watsi da karar da jam'iyyar ta PDP ta shigar ta neman a soke zaben na watan Fabrairu.

Kotun sauraron kararrakin zaben dai ta ce ta yi watsi da karar jam'iyyar PDP ne bisa gaza gamsar da kotun kan korafe-korafensu da suka hada da tafka makudi a zaben shugaban kasa da kuma ikirarin cewa shugaba Buhari bai cancanci tsayawa takarar ba bisa rashin mallakar shedar kammala sakandare.

Har wa yau, alkalan kotun sun ce jam'iyyar PDP ta kasa tabbatar da shaidun da ke nuna ita ce ta lashe zaben na shugaban kasa.

Sakamakon zaben na watan Fabrairu dai ya nuna Shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben da kashi fiye da 56 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Za a iya cewa ba wannan ne karon farko ba da ake samun takaddama a sakamakon zaben har a dangana da kotun koli ba, kasancewar duk lokacin da aka yi babban zabe wadanda ba su gamsu da sakamako ba kan garzaya zuwa kotun domin neman hakki.

Shi kansa Shugaba Buhari ya sha kalubalantar zabuka a baya lokacin da yake bangaren hamayya.

To sai dai wani abin dubawa shi ne ba a taba samun yanayin da aka soke zaben shugaban kasar a Najeriya.

Bayanan hoto,

A halin yanzu Shugaba Buhari ya tafi kasar Saudiyya kuma zai zarce Burtaniya