Firaiministan Lebanon ya yi murabus kan zanga-zanga

Hariri

Firai ministan Lebanon Saad Hariri ya ce zai yi murabus daga mukaminsa sakamakon zanga-zangar da aka kwashe makonni biyu ana yi a fadin kasar.

Zanga-zangar da ake yi a fadin Lebanon ta biyo bayan yunkunrin gwamnatin wanda ta janye na sanya haraji a kan kiran waya ta manhajar WhatsApp.

Kasar Lebanon na daga cikin kasashe da bashi ya fi yi musu katutu a duniya.

Zanga-zangar ta yi sanadiyyar rufe bankuna na kwanaki 10, baya ga wasu ofisoshi da makarantu da aka rufe sakamakon hakan.

A wani jawabi da ya gabatar ta gidan talbijin din kasar, Hariri ya ce zai mika takaradar aikin nasa ga shugaba Michel Aoun.

Saad Hariri ya ce "tsawon shekaru 13, al'ummar Lebanon sun yi dakon hanyar warware matsalar da kasar ke fuskanta Kuma na yi iya yina domin samo bakin zaren ta hanyar sauraran al'ummar kasa."

To sai dai duk da wannan jawabin da Hariri ya yi, masu zanga-zangar sun nuna rashin gamsuwa, inda suka ce =ba za su koma gida ba har sai dukkanin jami'an gwamnati sun yi murabus.