Ranar bugun jini: Abin da ya sa bugun jini ke karuwa a Najeriya.

Ranar bugun jini: Abin da ya sa bugun jini ke karuwa a Najeriya.

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron tattaunawr kan bugun jini

Likitoci sun ce akalla mutam dubu dari biyu, manya da masu karancin shekaru ne ke kamuwa da cutar bugun jini, da ke haddasa shanyewar jiki.

Mrs Rita Melifonwu shugabar kungiyar masu fama da shanyewar barin jiki a Najeriya, ta bayyana cutar a matsayin wadda kan kai ga rasa rai.

Yayin da ake tunawa da ranar fadakarwa kan cutar bugun jini ta duniya, Khalifa Shehu Dokaji, ya ttauna da Dr Suleiman Ibrahim Suleman, da ke asibitin Murtala Muhammad a Kanon, domin jin girman cutar a Najeriya.