Ana zargin dan Rasha da cin naman mutane

Tuni 'yan sandan Rasha suka garkame wanda ake zargi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mutumin da ake zargi ya zubar da kasusuwan mutanen da ya kashe

An cafke wani mutum a arewacin kasar Rasha tare da tuhumarsa da laifin cin naman mutum bayan gano wasu gawawwakin mutane da aka ci wasu sassan jikinsu, tare da sauran sassan jikin karnuka da magunan da su ma aka ci.

Ana zargin mutumin mai shekara 51 da hillatar mutanen uku ta hanyar kulla abota da su kafin daga bisani ya dirka musu barasa tare da kashe su da daddatsa namansu dannan ya fara cin sassan jikinsu.

Harwayau, an gano karnuka da maguna da wasu kananan dabbobi da suma ya ci namansu. An kuma gano kasusuwa a cikin wata katuwar jaka a kusa da wani kududdufi da ke kusa da gidansa a birnin Ar

Tuni mau bincike na Rasha suka fara gudanar da aiki dan bincikar mutumin, sun kuma wallafa bidiyon da suka dauka a shafin internet, yanayin wurin ya nuna an dauki bidiyon a inda ya ke cin naman mutanen.

Likitoci sun tabbatar da lafiyar kwakwalwarsa, an kuma gano daman tuntuni an taba kai rahoto kan wani laifi da ya aikata amma kuma hukumar tsaron FBI ta Rasha ba ta adana rahoto kan hakan ba.

Bincike ya nuna an kashe mutanen ne tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017, sai dai hukumar tsaron Rasha ta ce an dauki lokaci mai tsaho kafin a gano mutanen. Biyu daga ciki an kasa gano 'yan uwansu.

Mutumin da ake zargin dai ya kama hayar daki a gidan daya daga cikin mutanen da ya kashe, wanda daga bisani ya yi ikirarin ya tafi wani gari neman aiki. Ya shaidawa iyayen mutumin kafin ya yi balaguron ya amince da ya zauna a gidan dan ya kula da shi kafin ya dawo.