'Yan Democrat sun fito da sabon shirin tsige Trump

A draft

Asalin hoton, Reuters

'Yan jam'iyyar Democrat da ke majalisar wakilan Amurka sun wallafa wani kundi da ke zayyana mataki na gaba da za su bi a yunkurinsu na tsige shugaban kasar, Donald Trump.

Kundin dai ya kara fito da wani mataki ne na bukatar ci gaba da binciken da ake yi a kan Trump inda suke son mika kundin ga shugaban kwamitin bayanan sirri, Adam Schiff.

Zauren na majalisar wakilai dai wanda jam'iyyar ta Democrat take da rinjaye, zai kada kuri'a dangane da matakin a ranar Alhamis.

Wani mai magana da yawun fadar White House ya bayyana matakin da "haramtacce al'amari".

Tuni dai ake ta zaman jin bahasi a asirce.

Ana dai zargin Mr Trump da matsa wa kasar Ukraine lamba a kan binciken rashawa da cin hanci da ake yi wa abokin hamayyarsa, Joe Biden da dansa wanda ya yi aiki a kamfanin gas na Ukraine, Burisma.

Mr Trump dai ya ki amince wa da aikata ba dai-dai ba inda kuma yake yawan bayyana yunkurin tsige shi da bita-da-kullin siyasa.