Shin ko cutar Asthma na gurbata muhalli?

  • Daga Michelle Roberts
  • Health editor, BBC News online
girl using an inhaler

Asalin hoton, Getty Images

Mutane da yawa da ke fama da cutar Asthma na iya rage fitar da iskar Carbon dioxide don taimaka wa muhalli ta hanyar sauya magungunansu zuwa wadanda ba sa gurbata muhalli, in ji wasu masu bincike a Birtaniya.

Sauyawar za ta yi tasiri sosai ga muhalli.

Ba don komai ba, sai don abin shaka na masu Asthma na fitar da iska da ke janyo dumamar yanayi.

Amma tawagar ta Jami'ar Cambridge ta ce dole ne masu lalurar su tuntubi likitocinsu kafin su sauya magungunan.

Wadanne abin shaka ne ba sa gurbata muhalli?

Sama da mutane miliyan biyar ne su ke da cutar Asthma a Birtaniya.

Binciken ya duba tasirin da abin shakar yake yi a kan muhalli a Ingila.

A shekarar 2017, likitoci sun rubuta wa masu cutar abin shaka miliyan 50.

Bakwai cikin 10 da na abin shakar da aka bai wa marasa lafiyan, masu fitar da gurbatacciyar iska ce.

Ana amfani da iskar- mai suna Hydrofluoroalkane- wajen hankado iska daga cikin abin shakar.

Masu binciken sun yi kiyasin cewa abin shaka daya wanda ba ya bata muhalli zai rage yawan iskar Carbon dioxide da kiloton 58.

Wato kusan iskar Carbon da motoci 180,000 za su fitar idan suka je birnin Edinburgh daga Landan sannan su koma, a cewarsu.

Idan aka sauya Inhaler daya mai gurbata muhalli da marar gurbatawa, za a rage kusan kilogram 150 zuwa kilogram 400 a shekara.

Asalin hoton, Getty Images

Ko sauyawar na da amfani?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mutanen da ke da bukatar ci gaba da amfani da abin shakar mai fitar da gurbatacciyar iska na iya ci gaba da amfani da shi, in ji kwararru.

Sauyawa zuwa marar gurbata muhalli na iya jawo matsaloli ga masu cutar Asthma, saboda akwai abubuwan da yana da wasu sabbin abubuwa don haka dole a nemi taimakon likita ko malaman jinya.

Ga masu cutar da ba za su iya sauyawa ba, likitoci sun ce akwai wasu hanyoyi masu gyara muhalli da za a iya bi.

Shugabar kungiyar Asthma ta Birtaniya Jessica Kirby, ta bayar da shawarar cewa: "Yana da matukar muhimmanci ku ci gaba da abin shakarku yadda likita ya ce.

"Idan kuna da damuwa kan tasirinsa ga muhalli, ku yi magana da likitanku ko malaman jinya idan kun je asibiti, don ganin ko akwai wani abin shakar da za ku iya amfani da shi."

Shugaban NHS, Simon Stevens ya ce: Hukumar Lafiya ta riga ta rage yawan iskar gas din da take fitarwa da kusan kashi daya cikin biyar a shekaru goma da suka gabata.

Kuma sauyawa daga abin shaka masu gurbata muhalli zuwa wanda ba sa yi na cikin tsare-tsarenmu na dogon zango kuma zai taimaka wa doron kasa da mutanen da ke cikinta.